Masari ko Shema: Wane ne mai gaskiya?

Tun bayan gudanar da zaben ranar 11 Afrilun wannan shekarar wanda hakan ya yi sanadiyyar faduwar dan takarar dake samun goyan bayan Gwamnan jihar na wancan lokacin Barista Ibrahim Shehu Shema karkashin jam’iyyar PDP a Jihar Katsina. Kuma wanda ya mika ragamar mulki ga gwamna mai ci a  yanzu, wato  Rat. Aminu Bello Masari  na […]

Masari ko Shema: Wane ne mai gaskiya?
Masari ko Shema: Wane ne mai gaskiya?

Tun bayan gudanar da zaben ranar 11 Afrilun wannan shekarar wanda hakan ya yi sanadiyyar faduwar dan takarar dake samun goyan bayan Gwamnan jihar na wancan lokacin Barista Ibrahim Shehu Shema karkashin jam’iyyar PDP a Jihar Katsina. Kuma wanda ya mika ragamar mulki ga gwamna mai ci a  yanzu, wato  Rat. Aminu Bello Masari  na jam’iyyar APC.
Tun bayan wannan lokacin kafin ranar 29 Mayu Gwamna Shema na wancan lokacin ke ta kokari ganin ya wanke kansa akan kowace harkar rashin gaskiya, domin ya tsira da mutuncinsa, wanda abu ne mai wahalar gaske idan aka yi la’akari da yadda ya gudanar da gwamnatinsa.
A nasa bangaren Gwamna Aminu Bello Masari tun bayan darewarsa a karagar mulki ranar 29 Mayu ya maida hankalinsa, ya kuma jajirce a kan bincike da kuma fallasa almundahana da babakere da aka yi da dukiyar al’ummar jihar.
Babban abin lura a nan shi ne, mafi yawa daga cikin al’ummar jihar ba wannan binciken ba ne a gabansu, musamman idan aka yi la’akari da halin matsin da jihar ke ciki.
A jawabin cikarsa kwana 100 a karagar mulki Gwamna Masari ya ci gaba da kokawa akan yadda aka kwashe kudin jihar “karkaf” ta kowane bangare. Haka zalika shi ma tsohon Gwamna Shema ya ci gaban da kalubalentar zaben da aka yi wa  Masari a kotu, da kuma kare kansa game da zarge-zargen da ake yi masa, su kuma a nasu bangaren al’ummar jihar sun sa ido su gano wane ne mai gaskiya.
Su ma dattawan jihar da masu fada aji a jihar na ganin wannan fito-n- fito din ba zai haifar da da mai ido ba a jihar. Kamata ya yi kowane bangare su maida wuka cikin kube, kuma a yi hakuri sannan a yafe wa juna, domin ci gaban jiharmu ta Katsina  da ma kasar mu Najeriya  baki daya.
Adamu Aliyu amo, Jihar Katsina. Sakataren kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina.
09036514747/09097300909.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50