Masari ya kaddamar da ’yan Keke Napep na yankin Funtua/dandume mazauna Abuja
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kaddamar da kungiyar masu tuka Keke Napep na yankin mazabar Funtua da dandume mazauna Babbar Birnan Tarayya Abuja, tare da Keke Napep guda 2 da baburan hawa guda 10, da dan majalisar mazabar Honarabul Muktar dandutse ya baiwa kungiyar. Gwamnan ya kaddamar da kungiyar ne a gidan gwamnatin […]
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya kaddamar da kungiyar masu tuka Keke Napep na yankin mazabar Funtua da dandume mazauna Babbar Birnan Tarayya Abuja, tare da Keke Napep guda 2 da baburan hawa guda 10, da dan majalisar mazabar Honarabul Muktar dandutse ya baiwa kungiyar. Gwamnan ya kaddamar da kungiyar ne a gidan gwamnatin Jihar Katsina da ke Abuja.
Da yake jawabi a wajen, gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga matasa su rike sana’a domin komai kankantar sana’a tana da matukar alheri. Sannan ya yaba wa ’yan wannan kungiya kan kokarin da suka yi, wajen kama sana’ar da suke rike da kansu da iyalansu.
Ya ce yana tare da wannan kungiya dari bisa dari. Don haka Ya ce zai bayar da duk wata gudunmawa da ya kamata ya bayar ga wannan kungiya.
A nasa jawabin dan majalisar wakilai ta tarayya na mazabar Funtua/dandume da ke Jihar Katsina Honarabul Muktar dandutse ya godewa dukan wadanda suka halarci wannan taro.
Ya yaba wa shugaban wannan kungiya Imam Ibrahim Awwal [Usama] kan kokarin da yake yi wajen jagorantar al’ummar yankin Funtua/dandume da ke zaune a Abuja.
Daga nan ya bai wa kungiyar tallafin Keke Napep guda 2 da baburran hawa guda 10 kuma yi bukaci ’yan kungiyar su hada kai su ci gaba da ayyukan da suka sanya a gaba.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar kuma Limamin masallacin gidajen ’yan Majalisar Tarayya da ke zone B, Apo Abuja Imam Ibrahim Awwal [Usama] ya bayyana cewa sun kafa kungiyar ne da manufar taimawa mutanensu don su dogara da kansu.
Ya ce duk wanda rashin lafiya ya same shi a cikin wannan kungiya, suna iyakar kokarinsu wajen ganin sun nema masa magani kuma suna nemowa duk dan wannan kungiya da aka zalunta hakkinsa. Kuma suna da niyar su nemi wasu gidaje a bayan unguwar Apo, da ke nan Abuja don kamawa mutanensu don sun hada su a wuri daya.
Ya ce wannan kungiya ba kan masu tuka Keke Napep ta tsaya kadai ba, domin ta samarwa al’ummar yankin Funtua/dandume ayyuka ’Yan sanda da Soja da sauran ayyuka a wurare daban daban a Abuja.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci wajen wannan taro sun hada da DIG Bala Uba Ringim da Sanata Ali Ndume da dan majalisar wakilai ta tarayya Alhassan Ado Doguwa da Sarkin Nupe da dai sauransu.