Masari ya umarci a rufe asusun jihar a bankuna

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin rufe asusun banki na jihar da na kananan hukumomin jihar. Gwamna Masari ya bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin da ta gabata ranar farko ta kama aikinsa bayan karbar ragamar mulkin jihar.  Umarnin na Gwamna Masari ya biyo bayan wani taro da […]

Masari ya umarci a rufe asusun jihar a bankuna
Masari ya umarci a rufe asusun jihar a bankuna

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin rufe asusun banki na jihar da na kananan hukumomin jihar. Gwamna Masari ya bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin da ta gabata ranar farko ta kama aikinsa bayan karbar ragamar mulkin jihar. 

Umarnin na Gwamna Masari ya biyo bayan wani taro da ya yi da shugabannin kananan hukumomin 34 a gidan gwamnati.
Har ila yau, a wurin taron nasu an tattauna batun takin zamani tan dubu 12 da tsohuwar gwamnatin Shema ta ce ta sayo don rarraba wa manoma.
Kazalika, Gwamna Masari a ranar Talata ya shaida wa Manyan Sakatarorin Ma’aikatun Jihar cewa, za su kare kansu a kan bayanan da aka bayar a cikin kundin bayanai na ayyukan tsohuwar gwamnati daga ma’aikatunsu tare da amsa tambayoyi daga ’yan kwamitin karbar mulki daga tsohuwar gwamnati, kuma za a yi haka ne a gaban manema labarai inji Gwamnan.