Masassarar Najeriya ta harbemu
Daga Mujaheed Naseer Kudan Tarihi shi ne rayuwa, fahimtarsa ko gane aukuwarsa ita ce gishirin rayuwar, aiki da abin da ya zo da shi, shi ne abincin rayuwar. Shi ya sa masana ke ikirarin cewa “duk wanda bai san abin da ya faru ba (a gidansu, ko unguwa ko kauye ko sasa) kafin a haife […]
Daga Mujaheed Naseer Kudan
Tarihi shi ne rayuwa, fahimtarsa ko gane aukuwarsa ita ce gishirin rayuwar, aiki da abin da ya zo da shi, shi ne abincin rayuwar. Shi ya sa masana ke ikirarin cewa “duk wanda bai san abin da ya faru ba (a gidansu, ko unguwa ko kauye ko sasa) kafin a haife shi, to tabbas bai san tarihin rayuwarsa ba,’ kuma haka zai kasance tamkar jariri,’ wato bai san komai ba. Shi kuwa jariri ai mun san ba kawai rashin sanin abin da ya wakana ba ne ya dame shi, a’a jikinsa da wawalwarsa da yanayin ginuwar rayuwarsa.
Da sanin tarihi za ka iya gane wane ciki jiya ta samu, kuma me ta haifa yau kuma da sanin tarihi za mu fahimci wadanne irin ’ya’ya za a samu gobe. Duk da yake shekaruna ba za su wuce 22 ba, kuma ba zan iya kiran kaina a matsayin tsarrar Najeriya ba, kamar yadda mahaifina zai kira kansa. Kasancewa an haifi mahaifina ranar da Najeriya ta samu ’yancin kai, kuma ya ba ni labarin abubuwa masu yawa da suka wanzu a zamaninsu. Mafi yawan lokaci idan ya ba ni labarin romon dimokuradiyya da suka sha da yadda aka yi musu gata a lokacin da suke makaranta, sai naji tamkar a wata kasa suka rayu. Na dade ina mamakin yanayin yadda suka gudanar da makarantarsu cikin jin dadi da kwanciyar hankali, amman mu kuwa ko oho.
Zan iya tunawa a jami’ar mu wani malami yana ba mu labarin rayuwar da suka yi a lokacin suna kanana, daga lokacin haihuwarsu zuwa lokacin da aka yi musu kaciya. Ni kuma na kada baki na ce da Malam “Jiya ba yau ba! Lallai Malam kun taso cikin mani’imciyar rayuwa kai da Najeriya tsararka. Mu kuwa da muka tsiro a daidai lokacin da Najeriyar ta fara kamuwa da masassara (daga 1985 zuwa 1995), masassarar ta harbe mu. Domin kuwa abin da zan iya tunawa shi ne a daidai lokacin da aka yi mana kaciyar, garinmu babu asibitin da likita zai mana shayi, ballantana wani abu wai shi da wutar lantarki ko ruwan famfo.
A gida aka giggille mu da askar wanzami tamkar yadda aka yi wa kakanninmu. Mun dai dan ci kajin ba laifi; maganar lantarki da asibiti kuwa ma iya cewa jiya i yau. Bambancin kawai bai wuce turakun da aka kakkafa mana daure da wayoyi ba, hasken kuma sai mako-mako kamar sauran yankunan karkara takwarorin namu. Haka batun yake ga ginin asibiti, amma kiwata lafiyar sai mai Naira. Ruwan famfo kuwa sai in mun yi katarin shiga birni daidai lokacin da yake kwarara.To, muna fata dai Allah ya warkar da Najeriya daga wannan masassara da take fama da ita. Idan kuma ciwon ajali ne, to Allah ya yi mata kyakkyawar cikawa. Malam kuma Allah ya kara tsawon rai amin!”
Haka malamin nan yayi murmushi ya ce: “Malam Mujahidu ke nan. Hakuri za ku yi don wannan kasar sai addu’a don kullum al’amura kara lalacewa suke yi.”
A shugabancin baya an gina tunanin ’yan Najeriya ne a matsayin mutanen da za su taso su gina kasa, su yi komai ba don amfanin kansu ba, sai don amfanin al’ummmar kasar nan. Kodayake nima zan iya cewa malaman firamaren mu sun ginamu da wannan tarbiyar. Don wajen 1996 zuwa 2000 lokacin ina ajin farko zuwa aji hudu na makarantar firamare, malaman mu sun yi kokari matuka don su ga mun tarbiyantu wajen son al’umma da gina kasa.
A wannan lokaci idan an tambayemu, me muke son mu zama sai ka ji kowa na fadar ra’ayinsa. Kamar ni a lokacin ina cewa ne, ina son na zama likita mai taimakama wa al’umma. Wani kaji yace yana son ya zama Dan Sanda mai kare Kasa, Malami mai horror da dalibai ko kuma Dan Jarida maii taimakon al’ummma. Haka dai kowa ke fadar ra’ayinsa kuma a lokacin kowa burinsa ke nan amman sai kasha cikin kankanin lokaci tunaninmu ya sauya.
A kwanakin baya na samu wasu yara yan makarantar firamare nake tambayarsu me suke so su zama nan gaba. Sai daya yayi sauri ya ce shi yana son ya zama shuganan kasa ne, wani kuma ya ce gwamna.
Ya salam! To ya aka yi cikin kankanin lokaci tunanin kowa ya sauwa. Abin ba a yara kawai ya tsaya ba. Mu kanmu yanzu mafi yawan ‘yan ajinmu mun je muna karatu a inda muka san za mu samu kudi da yawa. Mafi yawa daga cikin mu basa tunanin kudin ta wace hanya zai fita ba; hallal ko haram?
Abuwa masu dadi sun faru lokacin da Najeriya take da shugabanni masu kishinta. Wutar Nepa da kiwon lafiya da makarantu da walwalar jama’a da sauransu. Amman mu a zamaninmu mun samu akasin haka. Idan ka ce za ka yi makaranta, to akwai yajin aiki, idan kasuwanci ne to kasa ba tsaro. Haka batun yake ga wadanda suka gama karatun don babu aikin yi. To yanzu me ake son dan kasar nan ya yi? Idan ka yi magana a ce baka da kunya, idan ka yi shiru a ce ba ka san ’yancin kanka ba. Idan ka yi zabe baka ganin abin da ka zaba sai abin da manyan mu suka zabar mana.
Matsalolin haka suke faruwa karuwa kullum. Amman a kowane hakuri akwai nasara, amma duk al’ummar da ta manta Allah, dole Allah ya manta da ita. Kowa zai iya gina rayuwarsa a, inda yake ganin ya da ce da shi amma mafi kyawun rayuwa ita ce rayuwa da tsoron Allah. Mu yi wa kanmu guzuri don mafi kyawun guzuri shi ne Imani. Allah ya tsare kasarmu da mutanen cikinta.
Mujaheed Naseer
dalibi ne a Jami’ar Jihar Kaduna, Sashen Koyon Aikin jarida (Mass Communication 200 lebel).
07035311650
[email protected]
www.mujaheednas.blogspot.com