Masha-Allah zabe ya yi kyau don an yi lami lafiya
Alhamdulillah! Kamar yadda mai karatu ya ji ya kuma gani, Allah cikin ikonsa ranar Asabar da ta gabata ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, ta fara gudanar da zabubbukan kasar nan.Zabubbukan da aka dade ana ta danbarwar za a yi, ko ba za a yi ba, bisa ga kokarin bullo da […]
Alhamdulillah! Kamar yadda mai karatu ya ji ya kuma gani, Allah cikin ikonsa ranar Asabar da ta gabata ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, ta fara gudanar da zabubbukan kasar nan.Zabubbukan da aka dade ana ta danbarwar za a yi, ko ba za a yi ba, bisa ga kokarin bullo da sabuwar Tazarcen da shugaba Jonathan ya yi tare da hadin bakin hedkwatar tsaro da wasu yan kanzaginsa na jam`iyyarsa taPDP, kai har ma da zugar `yan yankinsa na Neja Delta da ma wasu `yan sauran sassan kasar nan. Batutuwan da hedkwatar tsaron ta kawo shi ne farmaki da za ta fara kai wa a shiyyar Arewa maso Gabas da suke fama da rikicin `yan kungiyar Boko Haramyayin da `yan jamiyyar PDP da magoya bayan shugabaJonathan suka buge da cewa ba a kamala raba katuttukan kada kuri`a na din-din-din ba.
Waccan danbarwa ta sa ala tilas hukumar ta INEC a ranarAsabar 7-02-15, ta ba da shelar dage zabubbukan zuwa ranakun 28 ga watan Maris da kuma 11 ga wannan watan na Afrilu,maimakon 14 da 28 ga watan Maris da ya gabata.Alhamdulillah! Sai ga shi cikin ikon Allah, a ranar Juma`ar da ta gabata, wato ranar jajiberen fara babban zaben hedkwatar tsaronkasar ta ba da shelar cewa ta kwato garin Gwoza, hedkwatar karamar hukumar Gwoza da ke jihar Barno gari na karshe daya rage a hannun `yan kungiyar ta Boko Haram, inda nan ne kuma hedkwatar daular mulkin `yan kungiyar. Shi kan sa aikin rabon katuttukan kada kuri`ar na din-din-din an samu raba sama da kashi 84 cikin 100, a wannan lokaci da aka kara wa`adin zaben. A takaicen takaitawa dai Allah cikin ikonsa sai ga shi an tafi zabubbukan shugaban kasa da na `yan Majalisun Dokoki nakasa cikin kwanciyar hankali da lumana, an kuma yi su cikin son barka, in banda `yan tashe-tashen hankulan da aka samu a jihohin Ribas da Akwa Ibom da Enugu da Anambra.
Ko kusa bisa ga irin gangar da aka rika kadawa tsakanin `yan jam`iyyar PDP mai gwamnatin tsakiya da na babbar jam`iyyar adawa ta APC, ta zazzafan kalamai da cin mutuncin da kaskancin jinsi da kabila da cusa kiyayyar bambancin addini da kabila da uwa uba barazanar zubar da jini da ma ta za a yi yaki da wasu `yan kabilar Ijaw ta shugaban kasa Jonathan suka rika barazanar za a yi, muddin shugaba Jonathan ya fadi zaben, sun sa akasarin `yan kasa cikin fargabar ba za a yi zabubbukan lami lafiya ba kamar yadda aka yi zato ba. Amma dai ba salin-alin aka yi zabubbkan ba don kuwa rahotanni sun tabbatar cewa an yi harbe-harbe da saka bam a jihohi irinsu Enugu da Akwa Ibam daAnambra, baya ga ofishin jam`iyyar APC da aka kona a jihar Ribas. Duka-duka zuwa yanzu hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa a cikin rahoton da ta bayar bayan wannan zaben farkon cewa ta yi mutane 50, suka mutu tunda kakar zaben banan ta fara kadawa a bara. Laifuffukan magudin zabe irin na sace akwati ko cika shi da kuri`ar iska duk sun ragu matuka idan akakwatanta da na zabubbukan baya.
Wani abin sha`awa da godiya ga Allah a zaben, shi ne irin yadda `yan gudun hijira da rikicin `yan kungiyar Boko Haram yarutsa da su har suka bar garuruwansu da gidajensu daga jihohin Barno da Yobe da Adamawa su sama da miliyan uku sun samu kada kuri`unsu a sansanan da suke a dukkan fadin kasar nan, ba kuma tare da an samu tashin bam ko kai hari a irinwadannan jihohi ko sauran sassan kasa kamar yadda aka rika yin fargabar samu kafin ranar fara zabubbukan ba.
Hatta kayin zaben da gwamnonin jihohin Binuwai da na Neja da na Bauchi da na Kebbi (dukkansu gwamnonin PDP) suka shaa cikin takarar neman mukamin `yan Majalisar Dattawa da suka sha da ma irin yadda akasarin gwamnonin PDP suka kasa kawo jihohinsu ga shugaba Jonathan, duk Allah bai sa ka ji an tayar da wata husuma ba. A ganina wannan shi ne zabe mafi tsabta tun bayan zaben 1999, da sojoji suka mika mulki a hannun farar hula,duk kuwa da kasancewar shi ne mafi wahala a cikin tarihin mulkin dimokuradiyyar da kasar nan take kai yau shekaru 16.Abin da ya sa na kira shi mafi wahala, shi ne a zaben 2007,tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya so ya yi Tazarce kamar yadda shugabannin nahiyar Afirka suka saba yi amma ta faskara. Don haka aka samu canza mika mulkin shugabanci kasa a jam`iyya daya, wanda shi ne na farko irinsa atarihin kasar nan.
Bayan wannan canjin mulkin cikin gida da yanzu ya zama tarihi, sai kuma wannan canjin da aka samu a ranar Talatar da tagabata, a karon farko jam`iyyar adawa ta karbi gwamnati,bayan a baya jam`iyyun adawa a zaman dai-daiku sun yi ta yunkurin samun hakan tun daga zaben shekarar 2003 da na 2007da na 2011. Ba wai a kasar nan kadai ba a kusan dukkan nahiyarmu ta Afirka da Asiya inda nan ne har yanzu mulkin dimokuradiyya bai kankama da gindinsa ba, kamar yadda ya kafu a kasashe Turai da Amurka, duk kasar da ta kawo wannan matsayi a cikin mulkin dimokuradiyyarta, to, sai a fara taya ta murna, don ta fara kafa harsashin mulkin dimokuradiyya mai dorewa ke nan, kuma tana kokarin shiga cikin rukunin kasashen duniya da za a iya damawa da su a ko ina, wato ma`ana karantaya kai tsaiko ke nan.
Amincewa da sakamakon zaben da shugaba Jonathan ya yi na ya sha kayi, har ya yi karfin hali ya buga wa sabon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari wayar tarho ya taya shi murna, shi ma wani ci gaba ne kuma abin farin ciki a dimokuradiyyar kasar nan. Da wannan ke nan sai mu kara godiya ga Allah (SWT) da ya nuna mana irin wannan lokaci, mu kuma ci gaba da addu`ar Allah ya sanya zabubbukan da za a yi na gwamnoni da `yan Majalisun Dokoki na jihohi a ranar 11 ga wannan watan a yi su cikin kwaniyar hankali da lumana fiye ma da wannan. Ga shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari da jam`iyyarsu ta APC da sauran `yan kasa sai mu kara cewa Masha-Allah ,da aka yi zabe lami lafiya. Allah kuma ya kara ba mu kwanciyar hankali, karuwar arziki a kasar baki daya.