Mashaya uku
Wasu mashaya ne su biyu abokan juna, suka zauna gidan giya da maraice suna ta shan giya har dare ya yi sosai kuma kudinsu sun kare. Suka taho da niyyar zuwa gida, suna tafiya suna tambele da tunkudar juna; farin wata daren sha biyu, ko allura ka yar za ka tsinta. Nan gardama ta kaure […]
Wasu mashaya ne su biyu abokan juna, suka zauna gidan giya da maraice suna ta shan giya har dare ya yi sosai kuma kudinsu sun kare. Suka taho da niyyar zuwa gida, suna tafiya suna tambele da tunkudar juna; farin wata daren sha biyu, ko allura ka yar za ka tsinta. Nan gardama ta kaure tsakaninsu, har rana ta fito. daya na cewa farin wata ne ba rana ba ce, dayan kuma na cewa rana ce. A haka suka hadu da dan wiwi ya bugu, suka ce masa: “Don Allah Malam ka raba mana gardama, wai wannan hasken na rana ne ko farin wata ne?” dan wiwi ya kalle su ya ce: “Wallahi ni ma bako ne amma ku je gaba ku tambayi dangari.”
Daga Is’haka Sarkin Fulani Dankama, 08100006858