Mashayi

Wani mashayin wiwi ne, ya sha sosai ta shiga kansa sosai, kawai sai ya fasa kuka. Abokansa suka tambaye shi ko lafiya? Sai ya ce: “Wallahi ban ga kafarta ta dama ba.” Wani abokinsa mashayi ya daddage ya kasha shi da mari. Da ya ji zafi sai ya ce: “Yauwa, na gan ta wallahi.” Daga […]

Mashayi
Mashayi

Wani mashayin wiwi ne, ya sha sosai ta shiga kansa sosai, kawai sai ya fasa kuka. Abokansa suka tambaye shi ko lafiya? Sai ya ce: “Wallahi ban ga kafarta ta dama ba.” Wani abokinsa mashayi ya daddage ya kasha shi da mari. Da ya ji zafi sai ya ce: “Yauwa, na gan ta wallahi.”

Daga Ibrahim Hassan Gobir