Masoya ko masoyan Buhari?
Kusan shekara hudu da suka wuce na taba yin wani rubutu makamancin wannan game da masoyan Buhari da kuma kulafucin ganin ya ci zabe da irin bacin ran da wasu suka samu a lokacin da Buharin bai ci zaben ba. Abin da ya fi damuna a wancan lokaci shi ne yadda yawancin mutane suka yi […]
Kusan shekara hudu da suka wuce na taba yin wani rubutu makamancin wannan game da masoyan Buhari da kuma kulafucin ganin ya ci zabe da irin bacin ran da wasu suka samu a lokacin da Buharin bai ci zaben ba. Abin da ya fi damuna a wancan lokaci shi ne yadda yawancin mutane suka yi tagumi ganin cewa canjin da ake ta nema ya ki samuwa a maimakon a zage damtse a tabbatar da samuwar canji ko da Buhari bai hau karagar mulki ba.
Na sake dawowa kan wannan batu ne ganin cewa yanzu da Buhari ya ci zabe tagumi ya kare, canji ya fara samuwa, a wane matsayin kuma masoyan Buharin ke ciki yanzu?
Daga abin da ya faru a zaben da ya wuce da nasarar da Jam’iyyar APC ta samu an fahimci babban dalilin da ya sa aka samu nasara, ba kuma komai ba ne face ’yan Najeriya sun gano bakin zaren, ba yadda za su yi a daidai wancan lokaci su kara zaben Jam’iyyar PDP. Ba kuma wani abu ya jawo wannan turjiya ba, sai ganin cewa Jam’iyyar PDP wahala ce! Jam’iyyar PDP bala’i ce! Jam’iyyar PDP a daidai lokacin, rashin wutar lantarki da ruwan sha da rashin aikin yi ce! Yawancin mutanen kasar nan sun aminta da cewa Jam’iyyar PDP bakin mulki ce! Haka kuma an yi tarayya da cewa Jam’iyyar PDP talauci da rashin ingantaccen kiwon lafiya ce!
Idan mun tuna a daidai wannan lokaci ba irin abin da talakawa ba su fada ba. Wasu daga sashin talakawa na ganin cewa ta yaya za a yi a zabi irin wannan jam’iyya ta PDP da ta yi shekaru tana sa talaka cikin kunci da wahala. Saboda haka, tunda talauci da wahala da kunci bai san bambancin addini ba, talakawan Najeriya suka hadu suka canja wannan gwamnatin, yanzu sai labari.
Duk lokacin da ake ta wancan kokari, ina da tababa game da halin da mutanen kasar nan suke ciki da kuma irin yadda za su karbi canjin in ya samu. A cikin kundun zuciyata abubuwa da dama ke rayawa. Yawancin wadanda suka yi ta yekuwa da fafutikar kawo canjin, imaninsu ragagge ne. Haka kuma amanna da alwashin da ke tattare da su ragaggu ne. Kamar yadda na sha taunawa, ire-iren wadannan mutane, ni a nawa tunani MASOYAN Buhari ne.
A lura da abin da na jaddada, MASOYAN Buhari, ba MASOYA Buhari ba. Akwai bambancin tsakanin irin wadannan mutane. Me ya sa na ce haka! A halin da muke ciki duk wanda ka ji yana ta tunanin ai canji ya kusa samuwa, tun da Buhari ya ci zabe, ko ai ga shi mun fara ganin canji tun hawan Buhari, to MASOYIN Buhari ne, amma ba masoyin kawo canji ba. Irin su ne ke biye da akida da ruhi da tunani na irin gwamnatin da Buhari da irin aljannar da talaka zai shiga a lokacin da Buhari ya rashe kan karaga. Ma’ana, wanda bai ganin komai sai ci gaban da Buhari zai kawo wa Najeriya ba tare da duba zuwa ga irin tasa gudunmawar wajen kawo wa Najeriya canjin ba!
Irin wadannan mutane suna tare da Buhari a kowane irin fasali, amma sun bambanta da MASOYA Buhari. Ta yaya? Wadanda suke MASOYA Buhari, ba irin wadancan gungun da muka yi bayani a baya ba ne! Su MASOYA Buhari, su ne wadanda ke biye da akidojin Buhari da tunanin Buhari da tausayin Buhari da gaskiyar Buhari da kuma kima da daukaka ta Buhari! Akwai su kuma da dama a cikin kasar nan, wasu ba ma ’yan siyasar ba ne. Wasu ba kuma ’yan Jam’iyyar APC ba ne! Suna nan jibge! Irin wadannan MASOYA na Buhari ba su kallon Buhari a matsayin ma’asumi. Ba sa tsawwala wa jama’a idan sun kasance masu sayar da tumatir ko doya ko dankali ko shinkafa ko man gyada! Irin wadannan MASOYA na Buhari za ka gan su cikin kamala da da’a, ba wai haka nan sakayau ba, kamar dabbobi! MASOYAN Buhari ba sa neman kazamar riba! Ba sa cin mutunci ’yan uwa. Ba sa cin hanci da yin bocar iska a duk inda suke aikin gwamnati! Ba sa kuma yin algushu, idan an ba su kwangila! Ba sa gudun ganganci da kabu-kabu ko wani abin hawa, suna kashewa da gurgunta mutane a bisa titi! Ba sa ajiye mota ba bisa ka’ida ba! Ba sa zunde da gulma da zagin mutane! Ba sa yin dukkan wani abu da ba bisa ka’ida yake ba! Kai in gajarce maka, MASOYA Buhari ba sa nuna rashin da’a a kodayaushe! MASOYA Buhari masu gaskiya da rikon amana ne!
A halin da muke ciki akwai rikici tattare da nawa tunanin game da MASOYAN Buhari domin kuwa ban sani ba, in MASOYAN Buhari su masu gaskiya da rikon amana ne kamar sa! Shin muna jin cewa za mu iya barin Buharin da muke so ko mu taimaka wa Buharin da muke so ya yi aikin ci gaban kasar da ya kuduri aniyar yi? Ni dai ban sani ba!
Abin da na sani shi ne MASOYA Buhari, ba MASOYAN Buhari ba, su ne za su riki kasar nan da kyau har canji ya samu; kama daga mace mai sayar da man gyada zuwa kansila ko minista ko gwamna. Da Buhari ko ba Buhari! A ina kuke ku a halin yanzu, a wane matakin, na MASOYA Buhari ko kuwa MASOYAN Buhari?