Masoya sun yi aure bayan rabuwarsu da shekara 27

Wasu masoya ’yan kasar Filifins, Tomas Jun Tolentino da Rowena Weng Macaraeg, sun yi aure bayan shekara 27 da suka rabu da juna. Sanadiyyar rabuwarsu, rashin lafiyar da mahaifiyar Jun ta yi, don haka iyayensa suka yi kaura zuwa garin Samar da ke da nisan kilomita 800 a Kudancin Filifins.“Wannan al’amari ya auku ne a […]

Masoya sun yi aure bayan rabuwarsu da shekara 27

Wasu masoya ’yan kasar Filifins, Tomas Jun Tolentino da Rowena Weng Macaraeg, sun yi aure bayan shekara 27 da suka rabu da juna. Sanadiyyar rabuwarsu, rashin lafiyar da mahaifiyar Jun ta yi, don haka iyayensa suka yi kaura zuwa garin Samar da ke da nisan kilomita 800 a Kudancin Filifins.
“Wannan al’amari ya auku ne a lokacin babu wayar hannu, don haka muka kasa yin hulda da juna,” a cewar Weng, ’yar shekara 47. Da Jun ya bayyana bayan shkara, wato a shekarar 1986, tuni an daura wa Weng aure da wani abokin kuruciyarta, Carlito.
“Na dangana da halin da muka samu kanmu. Na kuma yi mata murna, saboda ta auri abokina,” a cewar Jun, dan shekara 49, inda ya kara da cewa ya ma halarci bikin auren abokinsa. “Ban yi bakin ciki ba. Na san ta shiga hannun nagari.”
Shi ma Juna ya samu mata, mai suna Winnie, wadda ta haifa masa ’ya’ya biyu, wadanda a halin yanzu shekarunsu 17 da 19.
Mijin Weng, carlito ya mutu a shekarar 2007, don haka ta zama bazawara. Shi ma Jun Jun Winnie matarsa ta mutu a shekarar 2009
A shekarar 2008, weng ta koma Dubai, ta kama aikin koyarwa a makarantar De la Salle Montessori  da ke garin Mankhool. Da ta tafi hutu a shekarar 2010, sai suka hadu da tsohon saurayinta a Manila, inda suka rika aike wa juna sakonnin tes; da sakonnin sadarwa na skype, har ta kai ga sun shirya bikin aurensu a dakin taro na kuezon City da ke Dubai, a ranar 22 ga Afrilun bara. Weng ce ta dauki nauyin Jun, inda suka tare a Dubai.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan