Masoyan mawaki sun yi zanga-zanga a Kano kan rashin fitar da sabon kundin waka

Mawakin ya ce yana alfahari da masoyansa, saboda a dalilinsu ne ya zama abin da ya zama a yanzu.

Masoyan mawaki sun yi zanga-zanga a Kano kan rashin fitar da sabon kundin waka

Wasu daga cikin masoya fitaccen mawaki a masana’antar Kannywood, Nura M. Inuwa, sun yi zanga-zanga kan rashin fitar da sabon kundin wakokinsa a bana, sabanin yadda ya saba yi duk shekara.

Masoyan dai sun yi zanga-zangar ne a ranar Litinin, da misalin karfe 1:30 na rana, inda suka yi tattaki zuwa ofishin mawakin dake kan titin Jami’ar Bayero, dauke da kwalaye.

Hakan ne ya sa Aminiya tuntubi mawakin ta wayar tarho, inda ya bayyana dalilinsa na rashin fitar sabbin wakokinsa.

Nura ya ce,

“Bayan zuwansu, na fito na kuma ba su hakuri kan rashin fitar wakokina ko sabon kundin waka.

“Tun a baya na sha fadar cewar yanzu zan koma sakin kundin waka duk bayan shekara-shekara.

“Kuma sun fahimce ni tare da yi min uzuri game da sabon salon da na dauka,” in ji Nura.

Wasu daga cikin masoyan mawaki Nura M. Inuwa yayin da suke gudanar da zanga-zangar lumana

Masu zanga-zangar, wadanda yawancinsu matasa ne na dauke da kwalaye wanda aka yi rubuce-rubuce a jikinsu.

Bayan zuwansu mawakin ya fito daga ofishinsa, inda ya musu jawabi tare da nuna jin dadinsa game da nuna kulawarsu a gare shi.

Ko a satin da ya gabata, mawakin sai da ya wallafa hotunan sakonnin wasu daga cikin masoyansa, kan yadda suke rokarsa a kan ya buga sabon kundin waka.

Wasu daga cikin masoyan Mawaki Nura M. Inuwa, mata yayin zanga-zangar kan rashin sakin sabon kundin wakarsa

‘Masoyana sun kafa tarihi’

Shi ma mawakin ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Instagram, inda yake cewa

“Karon farko a tarihin waka, a 2021 ni da ku mun kafa tarihi.

“Wannan zanga-zanga da kuka yi tana da ma’ana a wurina sosai, ta sani fargaba kuma ta sani farin ciki, saboda da ku na kafu na kai matsayin da ake labartawa,” cewar Nura.

Wasu daga cikinsu sun sa ran mawakin zai saki sabon kundi a watan Janairun 2021.

Amma mawakin ya jima yana ba wa masoyan nasa hakuri kan rashin fitar wani sabon kundin waka daga shi.

Amma a wannan karon ya musu albishir kan cewa nan da wani lokaci kadan zai saki sabon kudin wakokinsa.

Mawaki Nura M. Inuwa

Amma ya ce wannan sabon salo da yazo da shi, ya tabbata masoyan nasa za su yi farin ciki da shi.

Nura M. Inuwa, a yanzu ya fi mayar da hankali wajen buga wakokin biki da kuma wanda ake sa wa a cikin fim.

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54