Masu amfani da layin Glo za su samu kyautar kekunan dinki da Keke Napep a shirin Don Beta
Kamfanin Sadarwa na Globacom, ya fito da shirin bayar da kyaututtuka ga dubban mutanen da suke amfani da layukan wayar kamfanin, inda zai ba su damar samun garabasar kayayyakin da za su ingata rayuwarsu a karkashin shirin sanya kati a samu kyauta na My Own Don Beta. Garabasar wadda za ta sanya farin ciki a […]
Kamfanin Sadarwa na Globacom, ya fito da shirin bayar da kyaututtuka ga dubban mutanen da suke amfani da layukan wayar kamfanin, inda zai ba su damar samun garabasar kayayyakin da za su ingata rayuwarsu a karkashin shirin sanya kati a samu kyauta na My Own Don Beta.
Garabasar wadda za ta sanya farin ciki a zukatan miliyoyin masu amfani da layin Glo, tuni aka fara bayyana yadda za ta kasance ta kafafen sada zumunta na zamani da kafafen watsa labarai, kamar yadda kamfanin ya bayyana haka a babban ofishinsa da ke Ikko a ranar Alhamis din makon jiya.
Kamar yadda kamfanin ya tsara zai bi hanyar da ta dace wajen zaben kayyayakin garabasar da zai bai wa mutane.
Wani jami’in kasuwanci a Kamfanin Glo, Cif Dabid Maji, ya ce kayyayakin da za a ci sun hada da kekunan dinki da Keke NAPEP da injunan markade da kuma janaretoci da sauransu.
Ya ce shirin na My Own Don Beta ya fara ne tun ranar 3 ga Oktoban nan kuma ya hada da sabbabin abokan hulda da kuma tsoffafi.
Yadda za a shiga tsarin shi ne sai mutum ya sayi katin Glo na 200 ya sa a layinsa, “Yawan kudin da ka saka a layinka yawan damarka ta cin garabasa mai yawa,” inji Maji.
Maji ya ce dukkan masu amfani da layin Glo suna da damar cin wannan garabasa a fadin Najeriya, sannan wuraren da za a raba garabasar ga wadanda suka ci sun hada da Legas da Abuja da Fatakwal da Benin da Ibadan da Kano da Jos da Enugu da kuma Onitsha.