Masu bincike sun haƙo katako mai shekara 476,000 a doron ƙasa
Masanan sun ce ba su yi tunanin mutanen da suna da fasaha irin haka ba
Masu binciken kayan tarihi sun haƙo wani katako da aka yi ittifakin ya fi kowanne daɗewa mai kimanin shekara 476,000 a kan iyakar Zambiya da Tanzaniya.
Masanan sun haƙo katakon ne a ranar Laraba, inda suka ce hakan na nuna cewa mutanen da sun daɗe da wayewa fiye da yadda ake tsammani.
- An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Kano
- NNPP za ta daukaka kara kan hukuncin kotun kan zaben Kano
An dai gano katakon ne wanda aka yi wa kyakkyawar ajiya a kusa da ƙoramar Kalambo da ke kan iyakar kasashen biyu.
Binciken ya ce ana hasashen ajiyar mai wannan shekarun ta ma fi ɗan Adam daɗewa ke nan a doron ƙasa, kamar yadda masu zaben suka bayyana a binciken nasu a mujallar Journal Nature.
A jikin katakon dai har da wasu huje-huje da ke nuna wasu duwatsu da aka yi amfani da su da wasu guma-gumai guda biyu domin kera shi.
Kazalika, an kuma gano wasu kayayyakin a jikin katakwayen, ciki har da wasu sandunan haka a wajen.
An dai yi ittifakin halittun da suka gabaci mutane sun yi amfani da katako, amma ga wasu ayyukan da ba su wuce kunna wuta ko farauta ba.
Jagoran masu binciken, kuma malami a Jami’ar Liverpool da ke Birtaniya, Larry Barham, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa a iya sanin shi, katakon da ya fi dadewa a baya shi ne mai shekara 9,000.