Masu cutar coronavirus a Najeriya sun doshi 5,000
A Najeriya, an samu karin mutane 242 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a sa’o’i 24. Alkaluman baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar sun nuna cewa hakan ya kawo jimillar wadanda suka kamu a kasar zuwa 4,641. Hukumar ta ce a daren 10 ga watan […]
A Najeriya, an samu karin mutane 242 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a sa’o’i 24.
Alkaluman baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar sun nuna cewa hakan ya kawo jimillar wadanda suka kamu a kasar zuwa 4,641.
Hukumar ta ce a daren 10 ga watan Afrilu ta bada bayanan da suke ba daidai ba na adadin wadanda suka mutu a sakamakon cutar a jihar Nasarawa, inda ta nemi afuwa daga ‘yan Najeriya.
- Dage dokar zaman gida: Kare kai na yi wa mazauna Abuja wahala
- COVID-19: Jigawa ta killace almajirai sama da 30,000
“Mutum daya aka rasa a jihar Nasarawa, ba biyu ba kamar yadda muka fada a baya, muna neman afuwan gwamnatin jihar tare da tabbacin bada ingantattun bayannai.
‘zuwa tsakar daren Litinin adadin wadanda aka sallama ya tashi 902, yayin da wadanda suka mutu suka kai 150.
Galibin sabbin majinyatan dai, wato 88, a jihar Legas suke, 64 a Kano, 49 a Katsina, 13 a Kaduna.
Sai kuma jihar Ogun mai mutum tara, shida a Gombe, hudu a Adamawa, da kuma uku Yankin Babban Birnin Tarayya.
Yayin da jihohin Ondo, Oyo, Rivers, Zamfara, Borno, da Bauchi ke da mutum daya daya da suka kamu.