Masu dafa abincin aliban tsangaya sun yi bore a Jigawa

Ma’aikatan makarantar tsangaya da ke dafa wa alibai abinci sun yi wa karamar Hukumar Buji ta Jihar jigawa bore saboda gazawar ta wajan biyan su albashinsu na watanni bakwai. Shugabar matan masu dafa abinci a makarantar, Hajiya Amina Saleh, ta ce karamar hukumar tana ba su Naira 5,000 a kowane wata amma yau wata bakwai […]

Masu dafa abincin aliban tsangaya sun yi bore a Jigawa
Masu dafa abincin aliban tsangaya sun yi bore a Jigawa

Ma’aikatan makarantar tsangaya da ke dafa wa alibai abinci sun yi wa karamar Hukumar Buji ta Jihar jigawa bore saboda gazawar ta wajan biyan su albashinsu na watanni bakwai.

Shugabar matan masu dafa abinci a makarantar, Hajiya Amina Saleh, ta ce karamar hukumar tana ba su Naira 5,000 a kowane wata amma yau wata bakwai babu wadda aka ba koda sisin kwabo a matsayin albashinsu. Ta ce sun koka game da karancin runfa a lokacin damina da wurin fakewa idan hadari ya taso, ga rashin tsaro a makarantar; babu isassun masu gadi da suke kare lafiyarsu da ta yara a cikin makarantar. Don haka matan sun bukaci Gwamna Badaru da ya taimaka ya sa karamar hukumar ta biya su hakkokinsu.
Ta ce akwai bukatar gwamnatin jihar ta taimaka ta haa makarantar da wutar lantarki saboda rashin hasken wutar lantarki da karancin masu gadi ya sa a lokacin azumi da suke kwana a makarantar suna kwana ne a cikin larura.
Shi ma Babban Darakta a Hukumar Ilimin Baiaya, Malam Garba Bandi; ya tabbatar da hakikanin labarin. Ya ce makarantar suna sane da irin halin da suke ciki amma tuni aka bayar da aikin gyaran makarantar da katangarta ta zube da gyaran injin wuta da samar da rowan sha domin inganta rayuwar aliban makarantar.
Shi ma shugaban makarantar, Malam Sani Falalu, kokawa ya yi a kan matsalar rashin tsaro a makarantar da karancin ruwan sha da zubewar katangar makarantar. Ya ce rashin katangar ba karamar barazana ba ce a wajansa, kasancewar an danka masa kananan yara a hannunsa, domin lura da su.
Shi kuma Sakataren karamar Hukumar Buji, Malam Saleh A. Baba cewa ya yi maganar gaskiya karamar hukumar ta gaza wajan kasa biyan mata masu girki albashinsu na watannin bakwai amma suna nan suna kokarin biyansu. Ya ce yanzu haka sun tanadi albashinsu na wata aya kuma za su biya su.