Masu dauke da Coronavirus a Najeriya sun zama 214

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum biyar da aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, lamarin da ya sa yanzu jimillar wadanda suka kamu ya zama 214. A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce, “Zuwa karfe 10:10 na […]

Masu dauke da Coronavirus a Najeriya sun zama 214

Kwalba dauke da Sanfurin gwajin Coronavirus

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an samu karin mutum biyar da aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, lamarin da ya sa yanzu jimillar wadanda suka kamu ya zama 214.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce, “Zuwa karfe 10:10 na daren 4 ga watan Afrilu, akwai mutum 214 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Mutum uku daga cikin sabbin kamuwar a jihar Bauchi suke, mutum biyu kuma a Yankin Babban Birnin Tarayya.

An dai sallami mutum 25 da suka warke yayin da hudu suka rasu sanadiyyar cutar .