Masu dodo sun hana masu zaben Sarki sukuni a Zing
Masu bautar dodo na cigaba da cin karensu babu babbaka a garin Zing da ke Jihar Tabara bayan mutuwar Sarkin garin a watan jiya. Kimanin makonni uku ke nan masu bautar dodo suka mamaye fadar Sarkin Zing Marigayi Alhaji Abba Ibrahim Sambo wanda Allah Ya yi wa rasuwa a sakamakon turmutsutsin da ya faru a […]

Masu bautar dodo na cigaba da cin karensu babu babbaka a garin Zing da ke Jihar Tabara bayan mutuwar Sarkin garin a watan jiya.
Kimanin makonni uku ke nan masu bautar dodo suka mamaye fadar Sarkin Zing Marigayi Alhaji Abba Ibrahim Sambo wanda Allah Ya yi wa rasuwa a sakamakon turmutsutsin da ya faru a kasar Saudiyya lokacin aikin hajji, inda suka kori masu karbar gaisuwa tare da daukacin iyalan sarkin. An ce masu bautar dodon sun fasa dakin kwanan sarkin suka lalata daukacin kayan da ke dakin.
Binciken ya kuma nuna cewa masu bautar dodo sun tarwatsa masu zaben sarki ta yadda ba su kwana a gidajensu domin sun yi musu barazanar cewa idan ba su amince da sunan mutumin da suka ba su a matsayin sabon sarki ba za su kashe su, kuma sun hana jama’a cin babban kasuwar garin, wadda ke ci a duk rana Laraba, tare kuma da hana mata yin walwala a garin. Lamarin da ya tilasta wa wadansu mazauna garin, musamman Musulmi, kaurace wa garin tare da iyalansu don gudun kada a far masu.
Wata majiya a garin ta shaida wa wakilinmu cewa, har makarantu dole aka rufe su a garin domin tsoron gamuwa da fushin masu bautar dodon.
Majiyar ta bayyana cewa masu bautar dodo daga wadansu sassa na jihar da kuma jihar Adamawa su ma sun shiga garin na Zing inda suka mamaye daukacin garin da kuma fadar Sarkin, suka hana kowa sakat, duk da kasancewa ‘yan sandan kwantar da tarzoma da kuma sojoji
Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunasa don gudun kada a far masa, ya yi zargin cewa gwamnati jihar na da hannu a cikin mamayar da masu bautar dodon suka yi a fadar marigayi sarkin na Zing da kuma daukacin garin.
Ya ce abin mamaki ne ganin yadda masu bautar dodon suka wulakanta jama’a tare da lalata masallaci, amma babu abin da hukuma ta yi. Ya ce wannan ya nuna cewa gwamnatin jihar tana fifita wadansu mabiya addini fiye da wadansu. Ya yi zargin cewa, “da yake wadannan ’yan gatan gwamnati ne sai kawai aka sa masu ido, yau kusan kwana ashirin suna cin karensu babu babbaka.’’
Ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta binciki hukumomin ’yan sanda da na soja kan yadda suka bari aka cin mutuncin wadansu suna kallo ba su dauki mataki ba.
Gwamnatin jihar Taraba dai ba ta ce komai ba dangane da cigaba da kasancewar masu bautar dodon a garin na Zing da kuma yadda ake kyale su suke shiga cikin fadar Sarkin Zing suka ajiye kayayyakin tsafinsu.
Shugaban karamar hukumar Zing Malam Konko ya bayyana wa wakilinmu a lokacin da ya kira shi ta waya cewa, shi ba zai yi magana kan lamarin Zing ba, domin gwamnatin jihar ta hana shi yin magana.