Masu fyade da ’yan luwadi 369 sun shiga hannu a Katsina

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Aliyu Abubakar-Musa, ya ce ’yan luwadin da masu fyaden suna cikin masu laifi 1,627 da rundunar ta kama

Masu fyade da ’yan luwadi 369 sun shiga hannu a Katsina

‘Yan sanda

’Yan luwadi da masu fyade 369 ne dubunsu a cika ta Jihar Katsina a shekarar 2023 da muka yi bankwana da ita.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Aliyu Abubakar-Musa, ya ce ’yan luwadin da masu fyaden suna cikin masu laifi 1,627 da rundunar ta kama a jihar a shekarar.

Ya bayyana cewa rundunar ta kuma cafke mutane 176 kan aikata laifin kisa da kuma ’yan fashi da makami 258.

Abubakar-Musa ya ce runduar ta kashe ’yan bindiga 17, ta ceto mutum 171 da aka i gakuwa da su, da wasu 67 daga hannun masu safara bil’Adama.

A cewarsa, jami’an rundunar sun kwato bindigogi 12 kirar AK 47, harsasai 1,500, dabbobi 700, da motoci 12 da miyagun kwayoyi iri-iri daga hannun ’yan bindigar da suka shiga hannu.

Babban jami’in ya shaida wa manema labarai cewa wadanda aka gurfanar a kotu kan zarin aikata manyan laifuka sun kai 855, daga cikin 938 da aka samu a jihar a 2023.

Ya bayyana cewa nasara ta samu a sakamakon hadin dan da ke tsakanin rundunar da sauran hukumomin tsaro da ke aiki.

Da haka ya shawarci masu shirin aiakata laifi da su sauya tunani ko kuma su yaba wa aya zaki a hnunn rundunar.

Daga nai sai ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su ba wa rundunar da sauran hukumomin staro hadin kai, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna