Masu fafutika na neman’yancin giwar da ta shekara 40 a tsare

Masu fafutika hakkin dabbobi na neman ‘’yancin wata giwa da ta shekara 40 da kwacewa daga hannun mahaifiyarta, a kasar Filifins, inda take koyon kurme, sannan aka mika ta a matsayin kyauta ga tsohon Shugaban kasar Filifins, Ferdinand Marcos. Da tana zaune a daji mai ciyayi a kasar Sirilanka, amma aka mayar da ita a […]

Masu fafutika na neman’yancin giwar da ta shekara 40 a tsare
Masu fafutika na neman’yancin giwar da ta shekara 40 a tsare

Masu fafutika hakkin dabbobi na neman ‘’yancin wata giwa da ta shekara 40 da kwacewa daga hannun mahaifiyarta, a kasar Filifins, inda take koyon kurme, sannan aka mika ta a matsayin kyauta ga tsohon Shugaban kasar Filifins, Ferdinand Marcos. Da tana zaune a daji mai ciyayi a kasar Sirilanka, amma aka mayar da ita a kan falalen tandarkin sumunti a gidan namun dajin Manila, tun tana jaririya. 

Wannan giwa da aka yi wa lakabi da Mali, ta shafe shekaru 40 ba tare da ta ga mahaifiyarta ba, inda ta tare a wannan gidan namun daji tun a shekarar 1977. Kuma an fahimci cewa ba ta jin dadin gidan da aka ajiye ta.
Tsawon shekaru Mali ta samu matsalar tabin hankali, inda ta dugunzuma cikin bacin rai. Saboda zama a kan sumunti maimakon ciyayi da bishiyoyi. Tana fama da ciwon sanyin kashi da tafin kafa. Don ta samu saukin radadin ciwo takan makale a jikin bango. Tafukan kafarta dai sun tsattsage.
“Ina da tabbacin cewa Mali na fama da zafin ciwo a gabobinta da tafuka,” inji shi.
Wannan gidan namun daji bai yi komai ba wajen shawo kan matsalolin Mali. Kuma matukar ba nema mata magani ba, akwai yiwuwar ta gurgunce, ta yadda ba za ta iya tsayuwa ba. Da zarar nauyi ya danneta, to zai lalata sassan jikinta, har ta kai ga ta fadi ta mutu.
Gidan kyautata rayuwar giwaye na “Boon Lott’s Elephant Sanctuary (BLES)” da ke kasar Thailand ya bukaci a kawo Mali, domin a kula da ita, amma hukumomi a kasar Filifins sun ki amincewa.
Masu fafutikar hakkin giwaye sun samu nasarar kwatar ’yancin giwayen da suka hada da Sunder da Raju; ita Raju ma har shekara 50 ta shafe a tsare, kuma wannan namijin giwa ya samu ’yancin, inda ya tare a Mathura. Da yake giwa na iya rayuwa tsawon shekara 70, ana fatan ta kara shekara 10 a raye.
Masu fafutikar hakkin dabbobi, sun bukaci duk wanda ke wajen kasar Filifins, kuma ya damu da halin da Mali ke ciki, to ya rubuta wa jakadan Filifins wasikar neman taimako ga Mali. Kuma kuna iya tara kungiyar abokai masu irin wannan ra’ayi, don tunkarar ofishin jakadancin Filifins da ke kasar ku.