Masu fafutuka sun kai hari matatar mai a Iraki

’Yan Sunni masu fafutuka sun kai hari kan babbar matatar mai da ke Baiji a kasar Iraki.Sai dai ana samun rahotanni masu karo da juna da ke cewa masu fafutikar sun karbe iko da kusan baki dayan matatar bayan kashe masu gadinta.Amma wasu majiyoyi na gwamnati sun shaida wa gidan rediyon BBC cewa har yanzu […]

Masu fafutuka sun kai hari matatar mai a Iraki
Masu fafutuka sun kai hari matatar mai a Iraki

’Yan Sunni masu fafutuka sun kai hari kan babbar matatar mai da ke Baiji a kasar Iraki.
Sai dai ana samun rahotanni masu karo da juna da ke cewa masu fafutikar sun karbe iko da kusan baki dayan matatar bayan kashe masu gadinta.
Amma wasu majiyoyi na gwamnati sun shaida wa gidan rediyon BBC cewa har yanzu matatar man tana karkashin ikon dakarun tsaron kasar.
Rahotanni sun ce sojojin Iraki sun tura wani jirgi mai saukar ungulu mai bindigogi, inda jirgin ya rika harba makami mai linzami a kan wani tankin mai, abin da ya janyo gobara.
Hare-haren da mayakan sa-kan ke kaiwa inda suke ci gaba da dannawa zuwa birnin Bagadaza sun jawo Firayi Ministan Iraki, Nouri al-Maliki ya kori manyan hafsoshin sojan kasar hudu a ranar Talata sakamakon faduwar birnin na biyu a Iraki wato Mosul wanda ya fada hannun ’yan Sunni masu tada-kayar-baya a makon jiya.
Mutane a Bagadaza babban birnin Iraki na tara abinci da ruwan sha yayin da ake ganin ’yan tada-kayar-bayan na dada kusantar birnin.
Dakarun tsaron Iraki da sojan sa-kai ’yan Shi’a sun dakile yunkurin mayakan da kungiyar ISIS ke jagoranta a birnin Bakuba, mai nisan kilomita 60 daga Bagadaza.
Wani dan siyasa a birnin, Sa’ad Metalby ya ce sun amince a shigar da wani gagarumin kaso na mayaka ’yan sa-kai cikin dakarun soja da ke yankunan da suke kewaye birnin Bagadaza don tabbatar da cewa ba wani bako da ya shigo.