Masu fasa bututun man fetur sun shiga hannu

’Yan sandan musamman sun yi nasarra kame barayin man fetur da ke fasa bututun mai a yankin Ogijo a Jihar Ogun. ’Yan sandan na musamman suna aiki ne domin magance satar man fetur ta hanyar fasa bututu mallakar Kamfanin Mai na kasa (NNPC).Wadanda ake zargin sun hada da wasu tsafaffin tsagerun Jihar Ondo da wani […]

Masu fasa bututun man fetur sun shiga hannu
Masu fasa bututun man fetur sun shiga hannu

’Yan sandan musamman sun yi nasarra kame barayin man fetur da ke fasa bututun mai a yankin Ogijo a Jihar Ogun.
’Yan sandan na musamman suna aiki ne domin magance satar man fetur ta hanyar fasa bututu mallakar Kamfanin Mai na kasa (NNPC).
Wadanda ake zargin sun hada da wasu tsafaffin tsagerun Jihar Ondo da wani mamallakin wani sanannen gidan mai a garin Ogijo da daya daga cikin ma’aikatansa da wasu mutum biyar da ke satar fetur, wadanda aka kame a wurare daban-daban da suka a yankin  Shagamu da Ijebu Ode a Jihar Ogun.
daya daga cikin ’yan kungiyar tsagerun, Timi Tamarawemeyedo ya  ce ya bar inda suke yin muguwar sana’ar fasa bututun mai a Ikorodu, Legas ne sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakaninsa da shugabansu mai suna Ossy, wanda ya so ya kashe shi lokacin da ya nuna adawa da irin salon muguwar aikin nasa: “Mun fara samun baraka ne  lokacin da ya yi garkuwa da ’yan sanda tara a watan Mayun bara, la’akari da matsayina a kungiyar sai na bukaci da kada a kashe ’yan sandan, sai ya yi watsi da bukatar tawa; inda ya ba da umarnin kashe su bisa hujjar cewa suna kawo tsaiko ga aikace-aikacensa na fasa bututun mai. Hakan ne ya sa na baro wajen na dawo Ogijo, inda na ci gaba da harkokin da muka saba da wani dan uwana Austin Ajama, inda muka hada sabuwar kungiya da wasu mutanen yankin; wadanda suke da miyagun makamai,” inji Timi. Ya kara da cewa suna da injiniyan da yake taimaka musu mai suna Wasiyu, wanda yake fasa bututu ya gina musu kafar da suke karkatar da man fetur din.
A cewar Timi, dubunsu ta cika ne a daidai lokacin da wasu barayi suka sanya komar satarsu a bututun da injiniyansu, ya yi musu aiki, inda ’yan sanda suka far musu suka kame su ta hanyar taimakon babban dillalinsu Abdurahman Yusuf. Ya  ce ya sayi manyan motoci ya kuma gina gidaje na alfarma a Legas da Ondo, duk ta wannan muguwar sana’a.
Mai gidan man fetur a Ogijo wanda aka kama kan zargin sayen haramtaccen man fetur din, ya ce sau daya ya saya a cikin wasu jarkoki kuma ba ma shi ya saya ba, yaronsa ne da ke kula da harkokin gudanarwa ya sayi man a lokacin da nasu ya kare, lokacin ba ya nan, ya fita kasar waje.
A nasa bangaren, Abdulrahman Yusuf, ya ce yana sayar wa gidajen mai da dama man fetur, inda yake sayar musu da lita 50 a kan Naira 3,500 bayan ya sayo a kan Naira 3,000 daga masu fasa bututun.
Jagoran ’yan sandan CSP balentine Olumese ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifukansu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.