Masu fasa kwauri na ɗaukar hayar ’yan daba su kai mana hari – Kwastam

Za mu yi maganinsu ta hanyar ɗauka matakin da ya dace su fuskanci fushin doka.

Masu fasa kwauri na ɗaukar hayar ’yan daba su kai mana hari – Kwastam

Jami’an Kwastam

Hukumar Kwastam mai hana fasa kwauri a Nijeriya, ta ce wasu masu fasa kwaurin na ɗaukar hayar ’yan daba domin kai wa jami’anta hari.

Kwanturolan Kwastam na shiyya ta biyu, Dalha Wada Chedi ya ce masu fasa kwaurin suna kuma shirya zanga-zanga ba bisa ƙa’ida ba ga jami’ansa domin hana su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, kwanturolan ya gargaɗi irin waɗannan mutanen da cewa ba za su karaya ko hana jami’ansu gudanar da ayyukansu ba.

Ya bayyana cewa daga ranar 17 ga Fabrairu zuwa 28 ga Maris, 2024, shiyyar ta ƙwace kayayyakin da darajarsu ta kai Naira miliyan 769,465,907.46.

“Ina sanar da masu fasa kwaurin da ke ɗaukar hayar ’yan daba domin kai wa jami’anmu hari da shirya zanga-zangar da ba ta dace ba a kanmu cewa ba za su iya sa mu karaya da hana mu gudanar da aikinmu ba.

“Yana ɗaya daga cikin zaɓi biyu, ko dai waɗannan masu fasa kwaurin su juya wani sabon salo kuma su rungumi sana’a ta halal.

“Muddin ba haka ba kuma za mu yi maganinsu ta hanyar fuskantar fushin doka,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa shiyyar na amfani da haɗin gwiwar hanyoyin leƙen asiri masu inganci wajen yaƙar masu safarar shinkafa.