Masu fashi a tsakanin Adamawa da Gombe sun shiga hannu
’Yan sanda a Jihar Gombe sun kama barayin da suka addabi jama’a da fashi a kan iyakar jihohin Adamawa da Gombe. Da yake gabatar da barayin a gaban ’yan jarida a hedikwatar hukumar, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Mista Shino Olukolu ya ce sun yi nasarar kama barayin a kan iyakar jihohin Adamawa da Gombe […]

’Yan sanda a Jihar Gombe sun kama barayin da suka addabi jama’a da fashi a kan iyakar jihohin Adamawa da Gombe.
Da yake gabatar da barayin a gaban ’yan jarida a hedikwatar hukumar, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Mista Shino Olukolu ya ce sun yi nasarar kama barayin a kan iyakar jihohin Adamawa da Gombe tare da hadin gwiwar maharba da ’yan kungiyar bijilanti.
’Yan fashin sun hada da Sa’idu Adamu mai inkiya da Dujja, dan asalin kauyen Guyuk a Jihar Adamawa, dan shekara 35 da Ibrahim Mohammed mai inkiya da Yellow, daga karamar Hukumar Gerel a Adamawa, dan shekara 25. Akwai kuma Mobi Ori dan shekara 20 shi ma daga Guyuk da Kanno Dari daga Lamurde, dan shekara 30 da Hamza Isah daga Gerel, dan shekara 33 sai kuma Musa Ahmadu daga Lafiya Lamurde a Jihar Adamawa, dan shekara 30. Ya ce an kama su ne a sakamakon bayanan sirri da suka samu daga wasu mutane.
Ya ce ’yan fashin sun kware ne wajen tare hanya suna yi wa mutane fashi. Ya ce an samu bindiga kirar AK47 guda daya gidan harsashi guda 3 sannan da harsasai masu kyau guda 70 masu girman 6.9mm da karamar bindiga kirar, kirar Italiya. Sauran abubuwan sun hada da wayoyin salula guda shida da layu biyu da kuma wukake guda hudu.
Kwamishinan ya yi kira ga al’umma da cewa su ci gaba da bai wa ’yan sanda hadin kai da bayanai da za su taimaka musu. Daga nan sai ya ce za su dukufa wajen ganin sun zakulo sauran bata garin, inda ya ce jami’ansa na aiki ba dare ba rana na ganin sun kawo karshen ta’addanci a jihar.
Sannan ya ce da zarar sun gama bincike a kansu za su tura su zuwa kotu don yanke masu hukunci.