Masu filaye a wurin da za a gina garejin manyan motoci na Tafa sun nemi a biya su diyya

Masu filaye a daya daga cikin wurare biyu da aka killace don gina garejin manyan motoci a garin Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sun bukaci a biya su diyya kafin a ci gaba da aiki a wurin. Masu filayen wadanda suka bukaci a sakaya sunansu, sun bayyana wa Aminiya a Tafa bayan […]

Masu filaye a wurin da za a gina garejin manyan motoci na Tafa sun nemi a biya su diyya
Masu filaye a wurin da za a gina garejin manyan motoci na Tafa sun nemi a biya su diyya

Masu filaye a daya daga cikin wurare biyu da aka killace don gina garejin manyan motoci a garin Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sun bukaci a biya su diyya kafin a ci gaba da aiki a wurin.
Masu filayen wadanda suka bukaci a sakaya sunansu, sun bayyana wa Aminiya a Tafa bayan wata tawagar hadin gwiwa ta jami’an gwamnatin Jihar Kaduna da ta Tarayya ta je garin inda ta sanar da jama’a shirin fara aikin.
Sun bayyana cewa  tawagar ta sanar da su cewa gwamnatin Jihar Kaduna ta jinginar da wurin ga wani kamfanin kasar Amurka don gina garejin da sanya masa duk abin da ake bukata don gudanar da shi tare da karbar haraji na tsawon lokaci kafin mayar da shi ga gwamnatin a gaba. “Sai dai muna kira ga gwamnatin ta cika alkawarinta na ba mu diyya kafin fara aikin, inji su.
Sun ce garejin wanda za a gina a wurare biyu, daya a hannun tahowa daga Kaduna, dayan a hannun tahowa daga Abuja za su kasance a kusurowoyi biyu na shiga garin ne. “Sai dai tuni suka biya diyya ga masu filayen fitowa daga Kaduna wanda na gwarawa ’yan kasa ne, amma na hanyar fitowa daga Abuja har yanzu ba a ba mu diyya ba tukuna,” inji su.
Sun nuna takardun da suke dauke da sunayen masu filayen wadanda suka ce sun amsa ne daga karamar Hukumar Kachia kafin a kirkiro karamar Hukumar Kagarko daga baya.       
“Kuma kasancewar tun a lokacin gwamnati ta fitar da taswirar gini tuni wadansu daga cikinmu suka gina wurarensu amma duk sai aka bi aka rushe ba tare da an biya mu diyya ba sai muka ji yanzu an ba da wajen ga wani kamfani zai yi aiki saboda haka muna rokon Mai girma Gwamna Nasir El-Rufa’i ya sa a ba mu hakkinmu,” inji mutanen.