Masu fyade za su ji jiki a jihar Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta nuna damuwa dangane da yawaitar laifuffukan fyade da ake samu a sassan jihar, inda hakan ya sanya ta yi gyara a kan dokar fyade don yin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifi.Atoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Alhaji Ibrahim dantsoho ne ya bayyana haka, inda ya ce […]

Masu fyade za su ji jiki a jihar Katsina
Masu fyade za su ji jiki a jihar Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta nuna damuwa dangane da yawaitar laifuffukan fyade da ake samu a sassan jihar, inda hakan ya sanya ta yi gyara a kan dokar fyade don yin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifi.
Atoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Alhaji Ibrahim dantsoho ne ya bayyana haka, inda ya ce yanzu haka akwai karrarraki 21da suka shafi fyade a karamar Hukumar Katsina kadai.
Kwamishinan ya ce a cikin laifuffuka 10, akan tarar biyar sun shafi fyade ne ga kananan yara, inda ya yi kira ga iyayen yara da masu riko su kara sanya ido kan ’ya’yansu, kuma su rika kai rahoton aukuwar ire-iren wadannan laifuffuka ga hukumomi domin yin hukunci mai tsanani ga wadanda aka samu da fyade a jihar.
Alhaji Ibrahim dantsoho ya yi kira ga kafafen watsa labarai su rika bayyana irin hukuncin da ake zartarwa ga masu aikata fyade a jihar ta domin masu tunanin aikata irinsa su san irin tanadin da aka yi a kansu.