Masu gadi 3 sun shiga hannu kan aikata fyade

Taron dangi suka yi waje yi wa wadda lamarin ya shafa fyade.

Masu gadi 3 sun shiga hannu kan aikata fyade

Wasu masu gadi uku da suka hada kai wajen yi wa wata burduwa fyade sun fada a komar ‘yan sanda a Jihar Oyo.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya ce masu gadin na daga cikin mutum taran da aka kama da aikata laifuka daban-daban.

Da yake yi wa ’yan jarida karin haske a Ibadan, babban birnin jihar, Osifeso ya ce, “sai da suka karbe wa yarinyar wayarta sannan suka tsare ta a wani kebabben wuri har zuwa misalin karfe 1 na dare.

“Su ukun kowannesu ya yi lalata da yarinyar, sannan suka tilasta mata tura kudi (ta waya) zuwa wani asusun banki kafin suka tafi suka bar ta a wurin.

“Yayin bincike wadanda abin ya shafa sun yi na’am da zargin, kuma an kwace bindigar da suka ritsa budurwar da ita wajen aikata laifin da wayar da suka kwace a hannun ta,” in ji shi.

Daga cikin masu laifin da aka yi wa ‘yan jarida holensu har da wadanda suka aikata fashi da makami da garkuwa da fyade da sauransu.