Masu garkuwa da mutane sun sako Shugaban UBEC da ‘yarsa

Shugaban UBEC da Dokta Mohammed Mahmood Abubakar da aka sace tare da ’yarsa jiya Yasmin a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya kubuta ya kubuta. Idan ba a manta ba, a wata tattaunawa da Shugaban UBEC ya yi da wani dan uwansa da muka ruwaito dazun, an jiyo shi yana cewa duk inda za a nemo […]

Masu garkuwa da mutane sun sako Shugaban UBEC da ‘yarsa

Shugaban UBEC da Dokta Mohammed Mahmood Abubakar da aka sace tare da ’yarsa jiya Yasmin a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya kubuta ya kubuta.

Idan ba a manta ba, a wata tattaunawa da Shugaban UBEC ya yi da wani dan uwansa da muka ruwaito dazun, an jiyo shi yana cewa duk inda za a nemo kudin, a je a nemo domin a biya kudin fansansa da ’yarsa da aka yi garkuwa das u jiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A cewarsa, “Don Allah ku hanzarta. Lokaci na kurewa. Idan aka yi magana ka ga zai dauki wani dan lokaci kafin inda za a yi mhada a karba, kuma wannan abu ne in Allah ya yarda ana so a gama cikin awa guda. Don Allah su tartara duk abin da za su tattara cikin awa daya.”

“Amma wanda aka ce an samu daga Abuja, na san zai yi wuya a kai kudi daga Abuja zuwa Kaduna a daren nan. Ga 30 (miliyan ken an yake nufi) a kasa, ga 13 yanzu ya zama 43 ke nan. Suran 17. Don girman Allah duk inda za a samu a nemo.”

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos