Masu garkuwa da ɗan shekara 2 da ’yan uwansa na neman N300m
’Yan bindigar da suka sace yaro ɗan shekara biyu da ’yan uwansa mata uku a Kaduna na neman kuɗin fansa Naira miliyan 300 tare da barazanar halaka yaran
’Yan bindigar da suka sace yaron nan ɗan shekara biyu da yayyansa mata uku na neman kuɗin fansa Naira miliyan 300.
Sun kuma yi barazanar halaka ƙaramin cikin yaran saboda yawan kukansa.
Ɗaya daga cikin yaran marainiya ce, wadda mahaifinta wa ne ga mahaifin suaran ukun, waɗanda iyayensu ke kula da ita.
Masu garkuwar sun kira mahaifin yaran ne a ranar Alhamis suna neman kuɗin kafin su saki yaran, waɗanda babbar cikinsu ba ta fi shekara 14 ba.
- NAHCON ta mayar wa alhazai N5.3bn kan matsalolin Hajjin 2023
- NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen da iyaye ke fuskanta wajen tarbiyyar ’ya’yansu
Sun bukaci a biya kudin a ranar Alhamis ɗin, suna masu barazanar halaka su, idan ba a kawo kuɗin ba.
Mahaifunsu ya shaida mana cewa ya nemi sassaucin kuɗin, amma maimakon ’yan bindigar su amince sai suka fara duka yaran.
Ya ce, “sun kira ni suna neman kuɗin fansa, da na nemi su rage kuɗin sai na ji suna dukan yaran. Muna buƙatar addu’ar,” in ji mahaifin yara.
A ranar Laraba da misalin karfe 9 an dare ne ’yan bindiga suka sace yaran a gidansu da ke unguwar Keke A a yankin New Millennium City, da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Sun sace yaran ne a yayin da magidancin ya je dubiyar mahaifiyarsu da ke jinyar ƙannensu tagwaye a asibiti.