Masu garkuwa da dalibar BUK na neman N100m

An yi garkuwa da dalibar a kusa da unguwarsu a garin Kano.

Masu garkuwa da dalibar BUK na neman N100m

An yi garkuwa da wata dalibar Jami’ar Bayero ta Kano, Sakina Bello, a kan titin Janbulo zuwa Rijiyar Zaki da ke garin Kano.

Iyayen dalibar sun tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin da misalin karfe 3 na yammacin ranar Talata, yayin da take kan hanyar dawowa gida a cikin babur mai kafa uku, wanda ake kira da ‘Dansahu’.

Wadanda suka yi garkuwa da dalibar ta Jami’ar Bayero, sun tuntubi iyayenta a ranar Laraba suna bukatar a ba su Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan ta Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu rahoton bacewar dalibar da misalin karfe 3 na yammacin ranar Talata, kuma tuni suka fara bincike a kan lamarin.

Kiyawa, ya kara da cewa suna fadada bincike don gano inda wadanda suka yi garkuwa da ita suka boye ta.

A halin da ake ciki dai ba a riga an fara daukar darussa ba a Jami’ar Bayero, bayan dawowa daga hutun karshen shekarar karatu.

Amma tuni dalibai suka rajista domin komawa fagen fama da daukar darasi.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno