Masu garkuwa da mutane 10 sun shiga hannu a Taraba
Sojoji a Taraba sun kama gawurtattun masu garkuwa da mutane guda goma da suka addabi yankunan jihar da makwabta
Sojoji daga Birget na 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun kama wasu mutane goma da ake zargin masu sace mutane ne.
Mukaddashin kakakin rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya sanar da haka a ranar Talata.
Kyaftin Oni Olubodunde ya bayyana cewa daga ciki, sojoji sun yi nasarar kama wasu ’yan ta’adda takwas masu fashi da kuma sace mutane.
Ya ce wadanda aka kama su ne suka hana jama’a sakat a kananan hukumomin Wukari da Donga da Ussa da Takum tare da wasu yankunan Jihar Biniwai.
- Zanga-zanga: Majalisar Koli Ta Shari’ar Musulunci Ta Gargadi Matasa
- DAGA LARABA: Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama
“Binciken da sojoji suka gudanar ya nuna cewa dukkansu yaran wani kasurgumin dan ta’adda ne mai suna Terwase Akwaza wanda ake masa lakabi da suna Gana” in ji Kyaftin Oni.
Ya bayyana cewa uban gidan wadannan ’yan taaddan watau Gana, tuni aka kashe shi.
Kyaftin Oni ya kuma bayyana cewa an sami makamai tare da kayan sojoji da kudade a wajen ’yan ta’addan su takwas da sojojin suka kama.
Ya kuma bayyana cewa sauran ’yan ta’addan biyu daga cikin mutanen. an kama su ne a kauyukan Galeri da Kwodo da suke Karamar Hukumar Ardo-Kola bayan sun Sami bayanan sirri.
Kyaftin Oni ya ce an sami bindiga kirar AK-47 tare da harsasai a hannun wadanda aka kama.
Ya ce wadanda aka kama sun bayyana cewa su yaran wani kasurgumin dan ta’adda ne mai suna Kadogo Fun, wanda ya fitini al’ummar yankunan Bangalala da Kampani Zura da ke Jihar Filato.