Masu garkuwa da mutane 4 sun shiga hannu a Jigawa

Kazalika, rundunar ta cafke wani mutum da ya kware wajen kera bindiogi a jihar.

Masu garkuwa da mutane 4 sun shiga hannu a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta cafke wasu mutum hudu da take zargi da ta’adar garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Ringim.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce ‘yan sandan sun kuma kama wani mutum mai kera bindigogi.

Ya ce sun kwato bindigogi kirar gida guda uku, shanu 29, tumaki hudu, sarka daya da kuma babur kirar Boxer guda daya.

DSP Adam ya bayyana cewa, a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023, ‘yan sandan da ke aiki a sashen Ringim karkashin jagorancin Baturen ‘yan sandan yankin tare da hadin gwiwar ‘yan banga, suka kama mutumin mai shekara 50 da ke zaune a kauyen Yandutse Kawari, a Karamar Hukumar Ringim, wanda ya kware wajen kera bindigogi.

’Yan Najeriya 52,000 za su sauke farali a 2025

An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina

Tirela ta murƙushe ɗaliba har lahira a Bauchi

Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025