Masu garkuwa da mutane na cin karensu babu babbaka a Taraba

Masu garkuwa da mutane da barayin shanu sun addabi jama’ar wasu yankunan Jihar Taraba, inda binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa an sace fiye da mutum 11 a kananan hukumomin Gassol da Bali da Donga a ’yan kwanakin da suka wuce.Binciken kuma ya gano an sace shanu sama da dubu 17 kuma an […]

Masu garkuwa da mutane na cin karensu babu babbaka a Taraba
Masu garkuwa da mutane na cin karensu babu babbaka a Taraba

Masu garkuwa da mutane da barayin shanu sun addabi jama’ar wasu yankunan Jihar Taraba, inda binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa an sace fiye da mutum 11 a kananan hukumomin Gassol da Bali da Donga a ’yan kwanakin da suka wuce.
Binciken kuma ya gano an sace shanu sama da dubu 17 kuma an halaka makiyaya sama 150 a cikin shekara uku da suka wuce a kananan hukumomin Wukari da Ibbi da Bali da kuma Gassol.
Binciken ya nuna cewa a cikin wata biyu kacal an sace mutum shida a karamar Hukumar Gassol sai da ’yan uwan wadanda aka sace suka biya makudan kudi kafin aka sako su.
Wadanda aka sace a yankin Gassol sun hada da mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Jihar, Hajiya Belli Manu wadda aka sace ta a gidanta a garin Mutum-Biyu kuma sai da aka biya Naira miliyan 15 kafin a sako ta. Sai kuma Alhaji danladi da Alhaji Jido wadanda aka sace a garin Tella da ke karamar hukumar, inda aka ce ’yan uwan mutanen sun biya Naira miliyan takwas kafin a sako su.
Sai Alhaji Sahabi wanda aka sace shi a kauyensu na Chol duk dai a wannan karamar hukuma, shi ma sai da ’yan uwansa suka biya makudan kudi kafin a sako shi. Bayan haka an sace wasu mutum biyu a garin dan’ancha a karamar hukumar.
Sai kuma karamar Hukumar Bali inda aka sace mutum hudu wato Alhaji Ali Adamu Maibulawus da AlhajiAhmadu Bilkijo da Alhaji Abdulrasheed Adamu da Alhaji Alhaji Abdullatif Abdu Famri, inda ’yan uwansu suka biya miliyoyin Naira kafin a sako su. Sai kuma a karamar Hukumar Donga inda aka sace wani mutum a garin Bibinu kuma har yanzu ba a sako shi ba.
Wannan lamari kamar yadda bincikenmu ya nuna ya sa masu dukiya da ’yan kasuwa da manyan ’yan siyasa a kananan hukumomi zama cikin zullumi. Musamman ganin har zuwa yanzu ba wanda aka kama kan lamarin da ke dada karuwa.
Shugaban karamar Hukumar Gassol Alhaji Tukura Bashiru ya nuna damuwa kan yawan satar mutane a yankinsa, ya ce matsalar sabuwa ce a yankin amma sai ga shi ta zama ruwan dare a dan lokaci kadan.
Ya nemi jami’an tsaro su kara himma wajen gano masu aikata wannan mugun laifi.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Taraba Alhaji Sha’aba Alkali ya ce suna kokari matuka don gano masu satar mutane da shanu tare da sauran laifuffuka a jihar.