Masu garkuwa da mutane na cin karensu babu babbaka a yankin Giwa
Mutanen sun kara da cewa an sara musu kudi aka ce sai sun biya kafin a sako wadanda aka yi garkuwar da su, kuma an biya kudin amma sai aka sako dan Sarkin amma dan Alhaji Musa yau kusan kwana sittin ke nan babu labarinsa, har ma ta kai ga sun fid da rai da […]

Mutanen sun kara da cewa an sara musu kudi aka ce sai sun biya kafin a sako wadanda aka yi garkuwar da su, kuma an biya kudin amma sai aka sako dan Sarkin amma dan Alhaji Musa yau kusan kwana sittin ke nan babu labarinsa, har ma ta kai ga sun fid da rai da shi.
Kauyakun da suka yi makwabtaka da dajin Maidaru wanda ya yi iyaka da karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna da suka hada da kauyakan Kidandan da Sabon Birni da Kerawa da Karau-Karau da Galadimawa da Iyatawa sun koka a kan yadda ’yan bindiga ke kashe musu mutane tare da sace attajiran yanki suna garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Wakilinmu wanda ya ziyarci wasu daga cikin kauyaku ya iske jama’a da dama sun yi gudun hijira kamar kauyen Lamba da Kangon Kilishi da Kilishi da Walawa da Unguwar Kanawa da Unguwar Ayaba wadanda masu hali daga cikinsu suke ta barin kauyukan saboda gudun abin da ya faru da wadancan kauyuka kada su ma ya faru da su.
A zantawar da Aminiya da wasu daga cikin mutanen kauyakan wadanda suke cikin firgici da rudani a kan yadda ake kashe musu jama’a da yawancinsu ba su yarda a fadi sunayensu ko a dauki hotunansu ba saboda tsoron daukar rayukansu, sun ce an sace musu attajiran garinsu uku tare da kashe musu wani sarki da sauran wasu mutanen garin. Sun ce cikin wadanda aka sace kuma aka yi garkuwa da su, akwai wani mai suna Alhaji Musa Galadimawa wanda aka sace shi tare dan Sarkin Galadimawa. Kuma sun ce an kashe ’ya’yan Alhaji Musa su biyu magidanta tare da kwashe dukiyarsa har da babur dinsa.
Mutanen sun kara da cewa an sara musu kudi aka ce sai sun biya kafin a sako wadanda aka yi garkuwar da su, kuma an biya kudin amma sai aka sako dan Sarkin amma dan Alhaji Musa yau kusan kwana sittin ke nan babu labarinsa, har ma ta kai ga sun fid da rai da shi.
Sai kuma a kauyen Garke an kashe mutum uku aka kwashe dukiyarsu, sannan Alhaji Datti Bafulatani wanda shi ma mako uku da suka wuce aka sace shi, har yanzu babu labarinsa.
A kauyen Rafin Sarki an sace wani attajiri shi ma sai da danginsa suka biya kudi kafin a sako shi. Na baya- bayan nan shi ne na kashe Sarkin Kadage Malam Murtala Hayatu mai kimanin shekara 52 wanda aka yi a wayewar garin Lahadi da ta gabata.
Mutanen yankin sun shaida wa wakilinmu cewa wannan lamarin ya faro ne kwana sittin da suka wuce sanadiyyar tarwatsa ’yan ta’addar da suka addabi jihohin Kaduna da Neja da Katsina da Zamfara da Sakkwato da kuma Kebbi. Sun ce bayan an samu sauki tunda sojoji na ci gaba da sintiri a iyakarsu a karkashin wani soja mai suna Kyaftin Muhammadu, amma ana dauke shi daga wurin sai suka shiga halin ha’u la’i.
Mutanen yankin sun yi zargin cewa an dauke Kyaftin Muhammadu ne sakamakon wata takarda da wasu batagari suka rubuta cewa wai yana wuce gona da iri, sanadiyyar kashe wani da ake zargi da hannu a sace mutane da garkuwa da su, mai suna Alhaji Riskuwa danfulani. Sun yi zargin cewa kowa ya san Riskuwa ya yi kaurin suna wajen hada baki da sace mutane da kashe su da kwashe dukiyarsu, kuma wannan ne ya yi sanadin da ya sa aka kama shi aka kashe shi a garin Fatika.
Mutanen kauyukan sun ce har yanzu akwai wadanda suka zame wa yankin fitina kuma sanannu ne, “An san su akwai wani mai suna Ore da Iliya wadanda sanannu ne kuma fitinannu ne wadanda suke tare da Riskuwa wanda aka kashe amma su har yanzu ba su zo hannu ba,” inji daya daga mutanen yankin.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Zubairu Abubakar a kan abin da yake faruwa a yankin sai ya ce zai tafi masallaci bayan awa daya ya kira shi, amma ya kira har sau biyu bai dauki wayar ba.
Wakilinmu ya kira shugaban rundunar Operation Yaki Kanar Yakubu Yusuf Soja (mai ritaya) ta wayarsa amma ba amsa, amma wata majiya ta ’yan sandan yanki ta ce lallai ana fama da matsalar sace mutane ana garkuwa da su tare da kashe wasu daga cikinsu.