Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Maharan sun hana manoman yankin girbe amfanin gonarsu.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

’Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma shida, inda a halin yanzu suke neman Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.

Maharan sun kashe wani manomi, sannan sun sace wasu manoma guda shida a Ƙaramar Hukumar Bali a Jihar.

Rahotanni sun nuna cewar maharan, sun kashe wani manomi mai suna, Alhaji Mai Wanda Maibultu, a gonarsa a ranar Lahadi.

Maibultu sananne ne a wajen manoma a ƙauyen da ke kusa da garin Garba Chede.

An sace manoma guda shida ne a garin Garbatau, wanda yawancin mazauna garin manoma ne.

Wani mazaunin garin Maihula, Adamu Dauda, ya ce ’yan bindigar sun tuntuɓi iyalan waɗanda suka sace, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.

Ya kuma ƙara da cewar a irin wannan lokaci a bara, ’yan bindigar sun mamaye yankin, inda suka sace manoma da dama, sannan suka hana su girbe amfanin gonarsu.

“Yanzu haka, manoman na lokacin girbi, amma ’yan bindigar sun sake hana su girbe amfanin gonarsu, kamar yadda suka yi a bara.

Ƙoƙarin jin ta bakin bakin kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya ci tura, domin bai ɗauki waya ba.