Masu garkuwa da mutane sun bukaci Tabar Wiwi da Codeine a matsayin fansa

“Sun bukaci mu taho da katan din Codeine da Tabar Wiwi da ruwan sha da kuma abinci.”

Masu garkuwa da mutane sun bukaci Tabar Wiwi da Codeine a matsayin fansa

Maganin Codeine

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum uku a yankin Obada-Oko da ke Karamar Hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun.

Sun kuma sami nasarar harbe wani mutum daya a harin da suka kai ranar Asabar.

Tuni dai masu garkuwar suka tuntubi iyalan wadanda suka sace din, inda suke neman a basu Naira miliyan 10 da katan din maganin tari na Codeine da Tabar Wiwi da ruwan sha da kuma abinci kafin su sake su.

A cewar mazauna yankin, duk da musayar wutar da suka yi da ’yan sandan yankin, ’yan bindigar sun samu tafiya da mutum ukun.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, wani wanda ya kubuta daga harin, Razaq Lasisi, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa an kai harin ne a daidai lokacin da yake dawowa daga wajen aikinsa, da misalin karfe 9:00 na dare.

Razaq ya ce, “Masu garkuwar sun kira waya yau [Litinin] sun bukaci a basu Naira miliyan 10 kafin su saki mutanen.

“Sun kuma bukaci mu taho da katan din Codeine da Tabar Wiwi da ruwan sha da kuma abinci.

“To amma bayan doguwar tattaunawa, sun amince a basu Naira miliyan daya da rabi da Codeine da ruwa da kuma abinci,” inji shi.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ce tuni ma suka sami nasarar kama mutum daya bisa zarginsa da hannu a ciki, yayin da suke ci gaba da bincike don kamo ragowar.