Masu garkuwa da mutane sun kama liman da malami

Wadansu masu garkuwa da mutane sun kama wani limami daga garin Kubwa na yankin Abuja tare da wani malami da suke tare da shi a lokacin da suke dawowa daga garin Ibadan na Jihar Oyo, inda suka je wani taron Musulunci.  Limamin mai suna Shakurullah Badewa wanda jagora ne a wata kungiyar da’awa tare da […]

Masu garkuwa da mutane sun kama liman da malami

Wadansu masu garkuwa da mutane sun kama wani limami daga garin Kubwa na yankin Abuja tare da wani malami da suke tare da shi a lokacin da suke dawowa daga garin Ibadan na Jihar Oyo, inda suka je wani taron Musulunci. 

Limamin mai suna Shakurullah Badewa wanda jagora ne a wata kungiyar da’awa tare da Shakurullah Akindele sun gamu da jarrabawar ce a ranar Lahadin da ta gabata a kan hanyar Benin zuwa Lakwaja a kusa da wani gari mai suna Ibillo da ke karamar Hukumar Akoko-Edo da ke Jihar Edo, kamar yadda wata da suke tafiya tare da mutanen ta bayyana wa Aminiya.

Matar ta ce da farko masu garkuwa da mutanen wadanda suka cimma motarsu bayan wata ’yar tafiya daga wani shingen sojoji, sun bukaci su tsaya sannan bayan tsayawar tasu, sai suka tasa keyar malamin tare da abokin tafiyarsa zuwa cikin daji, suka bar ta a wurin tare da daya daga cikin matan limamin a jikin motarsu bayan sun amshe masu wayoyi.

Ta ce bayan wani dan lokaci wadansu sojoji sun je inda suka tsaya, sannan suka wuce da su zuwa sansaninsu, kafin daga bisani suka jagorance su zuwa wani babban ofishin ’yan sanda na yankin inda suka ba da bayani a kan lamarin, sannan suka yi musu hanyar dawowa gida Kubwa tare da motarsu.

Wasu bayanai da suka kara fitowa a shekaranjiya Laraba sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci makusantan mutanen su ba su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa. S ai dai a cewar wata majiya a karshe sun rage adadin zuwa Naira miliyan 10. Haka kuma lamarin ya sanya mutanen yankin cikin alhini, inda aka bukaci jama’a a masallatai su gabatar da addu’o’i na musamman kan Allah Ya sanya tausayi a zukatan masu garkuwan da su, su sako su ga iyalansu ba tare da yi musu wani lahani ba.