Masu garkuwa da mutane sun kashe dan majalisa bayan sun karbi miliyan 25
Masu garkuwa da mutane sun kashe dan majalisar dokokin jihar Taraba, Hosea Ibi bayan sun karbi kudin fansar Naira miliyan 25 daga iyalansa. An sace dan majalisar tun ranar 30 ga watan Disemban shekarar 2017 a gidan mahaifiyarsa da ke garin Takum. Aminiya ta gano cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin […]

Masu garkuwa da mutane sun kashe dan majalisar dokokin jihar Taraba, Hosea Ibi bayan sun karbi kudin fansar Naira miliyan 25 daga iyalansa.
An sace dan majalisar tun ranar 30 ga watan Disemban shekarar 2017 a gidan mahaifiyarsa da ke garin Takum.
Aminiya ta gano cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansar Naira miliyan 75 da farko amma sai iyalansa suka nemi su biya miliyan 30 daga bisani kuma suka rage kudin zuwa miliyan 25.