Masu garkuwa da mutane sun kashe DPO a Abiya
Aranar Litinin da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas ta sanar da kashe wani babban jami’inta da wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne suka yi masa kwanton bauna suka sace shi kafin daga bisani a tsinci gawarsa a gefen titi. Bayanai da Aminiya ta ruwaito na nuni da cewa jami’in ‘yan […]
Aranar Litinin da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan Jihar Ribas ta sanar da kashe wani babban jami’inta da wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne suka yi masa kwanton bauna suka sace shi kafin daga bisani a tsinci gawarsa a gefen titi. Bayanai da Aminiya ta ruwaito na nuni da cewa jami’in ‘yan sandan DPO ne na Gundumar Rumuorlumeni mai suna Kingsley Chukueggu.
Lamarin ya faru ne kamar yadda Aminiya ta samu labari, cewa DPO Chukwueggu ya hadu da ajalinsa ne a kan hanyarsa ta zuwa wani gari Owazakusa dake Jihar Abiya, bayan da ya baro Fatakwal, inda wasu da ake zaton cewa masu kama mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa ba tare da sanin ko waye ba, suka kama shi suka shiga da shi kungur min daji, kafin daga bisani su kashe shi su yasar da gawarsa gefen hanya, inda jama’ar wannan yanki masu wucewa su sanar da hukuma abin da ya faru, da aka zo aka ga ashe jamai’in dan sanda ne.
Marigayin mai mukamin Sufuritandan (SP), wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar, Nnamdi Omoni, inda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma kara da cewa ya zuwa lokacin amsa tambayoyin wakilin namu, babu wani wanda aka kama kan zargi, sai dai suna nan suna bakin kokari na bincike domin gano wadanda suka aikata wancan danyen aiki in ji shi.