Masu garkuwa da mutane sun kashe mutum 9 a Kamaru
An tsintsi gawawwakin wasu mutane tara a yashe a wani daji a karamar Hukumar Diir da ke lardin Adamawan Kamaru.Gabanin mutuwarsu, mutanen an yi garkuwa da su tun makonni biyu da suka gabata ne. Akasarinsu matasa ne makiyaya daga kabilar Mbororo da Gbaya. Bayan garkuwar da suka yi da tarin jama’a, sai masu garkuwar suka […]
An tsintsi gawawwakin wasu mutane tara a yashe a wani daji a karamar Hukumar Diir da ke lardin Adamawan Kamaru.
Gabanin mutuwarsu, mutanen an yi garkuwa da su tun makonni biyu da suka gabata ne. Akasarinsu matasa ne makiyaya daga kabilar Mbororo da Gbaya.
Bayan garkuwar da suka yi da tarin jama’a, sai masu garkuwar suka zabi sakin wasu daga ciki domin su shigo gari su ba da bayani game da kudin fansar da suka nema daga wurin mutanen da suke garkuwar da su. Har ila yau, sun isar da sakon jan kunne wanda maharan suka aiko wadanda suka saka da shi. Wannan ya sa jama’ar garin suka shiga wani hali na firgici.
Lamarin da ya sa jami’an tsaron Bataliyar kai daukin gaggawa tare da takwarorinsu masu sintiri da motoci suka bazama daji wurin bin sawun maharan. Sai dai har lokacin da wa’adin da wadannan mahara suka deba wa masu biyan kudin fansa ya cika ba su bayyana ba. Daga nan ne suka yanke shawarar hallaka wadannan matasa. Sai dai abin da ba a sani ba shi ne wadannan maharan ba su bayyana adadin kudin da suke bukata domin su saki matasan ba. Har ila yau, ba su fadi wurin da za a je a hadu da su domin su karbi kudin da suke da bukata ba.
Lardin Adamawan Kamaru ya dade yana fama da batun rashin tsaro, inda fashi da makami da ake kira “Zargina” shekaru da dama gabannin bullowar kungiyar Boko Haram wadda har a yanzu ta’addancin da take haddasawa a Kamaru bai shafi lardin Adamawa ba duk da cewa yana yankin arewacin kasar.