Masu garkuwa da mutane sun sace Limaman Kirista uku a Kaduna
Wasu da ake zargin masu satar mutane ne suna garkuwa da su domin samun kudi sun sace wasu Limaman Addinin Kirista uku ciki har da Rabaran Emmanuel Dziggau, Shugaban cocin United Church of Christ in Nigeria.Bayanai sun ce ’yan bindigar sun yi wa cocin da ke titin Kaduna zuwa Abuja dirar mikiya ne a ranar […]
Wasu da ake zargin masu satar mutane ne suna garkuwa da su domin samun kudi sun sace wasu Limaman Addinin Kirista uku ciki har da Rabaran Emmanuel Dziggau, Shugaban cocin United Church of Christ in Nigeria.
Bayanai sun ce ’yan bindigar sun yi wa cocin da ke titin Kaduna zuwa Abuja dirar mikiya ne a ranar Litinin da ta gabata da safe, inda suka sanya kyalle suka rufe fuskokinsu kafin suka dauke shugaban cocin da mabiyansa biyu.
Aminiya ta samu labarin cewa mabiya cocin da suka ga abin da ya faru sai suka ruga cikin dajin da ke kusa domin tsira da rayukansu.
Babban Sakataren Cocin, Rabaran Jibrailu Wobiya ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce Rabaran Dziggau da sauran mabiya sun isa cocin ne da nufin duba yadda ayyuka ke tafiya, saboda shirin da suke yi na shirya bikin addu’o’i a wurin.
Ya ce shi da sauran mabiya cocin sun ruga cikin daji ne domin tsira da rayukansu, inda ya ce ’yan bindigar sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 kafin su sako mutanen nasu.
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Jihar Kaduna, Rabaran George Dodo ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya roki jami’an tsaro su tabbatar sun kwato shugaban da sauran daga hannun matsaransu.
“Ya kamata gwamnati ta bai wa dukkan jami’anta umarnin tabbatar da an gano inda suke domin kubutar da su daga hannun masu garkuwa da su,” inji shi.
kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Zubairu Abubakar ya ci tura domin bai amsa waya baa A wani labarin Kwamandan Rundunar Soji ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar Adeniyi Oyebade ya ce sojoji sun kashe ’yan bindiga da barayin shanu 35 a jihohi biyar da ke jihohin Arewa maso Yamma.
Janar Oyebade ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya ce sojojin sun kuma yi nasarar kwato shanu dubu shida da tara daga maboyar barayin shanun.
Janar Oyebade wanda ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema Labarai, ya ce sojojin sun kama barayin shanun akalla 39 a cikin dazuzzukan jihohin biyar.
Ya ce rundunar ta kafa wani rukuni mai suna Operation Sharar Daji, da ke gudanar da aiki a jihohin Kaduna da Kano da Katsina da Zamfara da kuma Neja. “Mun yi aiki a Jihar Kaduna cikin dajin Damari a Birnin Gwari da Kwalakwange. Mun rusa maboyar barayin shanu. Mun halaka wasu sannan muka kwato dabbobi masu yawa. Makaman da muka kwato daga hannunsu sun hada da bindigogi kirar AK 47, biyu, da karamar bindiga daya da wukake da kwari da baka da Naira dubu 45. Sannan sojoji uku sun samu rauni, daya ya rasu,” inji shi.