Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 13 a yankin Kurama
Sarkin Kurama da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Dokta Ishaku Sabo Damina ya ce masu garkuwa da mutane da suka addabi yankin, sun sace mutum 13 sun tafi da su suna neman sai an biya su kudin fansa kafin su sako su. Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da […]

Sarkin Kurama da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna Dokta Ishaku Sabo Damina ya ce masu garkuwa da mutane da suka addabi yankin, sun sace mutum 13 sun tafi da su suna neman sai an biya su kudin fansa kafin su sako su.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce masu satar mutanen da ake kyautata zaton barayin shanu da aka koro daga dajin Birnin Gwari da Kachiya da Jere ne suka dawo dajin Kudaru da ke yankin suke aikata haka. Ya ce dajin babba ne wanda yake kunshe da duwatsu masu lungu-lungu da barayin suke shiga su buya.
Sarkin ya ce a kwanakin baya barayin mutanen sun shiga garin ’Yarkasuwa suka je gidan wani dan kasuwa mai sayen shanu, suka kwace Naira miliyan daya da dubu 700. “Bayan haka sun sake shiga garin suka samu wata mai sayar da giya, suka kwace mata Naira miliyan daya da dubu 200. Kuma sun sake samun wani Ibo dan kasuwa suka kwace masa kudi a garin. Sai Ranar Lahadin da ta gabata suka sake dawowa garin da misalin karfe 1:30 na dare, suka bude wuta da bindigogi suka koma wurin matar da suka kwace wa kudi kwanakin baya, suka kama wata mai suna Maman De suka tafi da ita. Sannan suka koma gidan mai sayen shanun da suka kwace wa kudi, suka dauke matarsa da take goyon yarinya ‘yar shekara daya da watanni suka bar goyon suka tafi da ita,” inji Sarkin.
Sarki Damina ya ce duk wadanda suka sace su kan kai su cikin duwatsun dajin Kudaru, sannan su fadi kudin da suke son a biya su, kuma ana zuwa dajin a kai musu kudin. “Zuwa yanzu sun sace mutum 13 a masarautata, kuma kusan dukkan wadanda aka sace din Fulani ne. Fulani da dama sun gudu sun bar rugagensu a masarautar saboda sace-sacen mutane da ake yi,” inji shi.
Ya ce roki hukumomin tsaro su turo jami’ansu su shiga cikin duwatsun dajin Kudaru domin kamo barayin a kore su daga wurin.
Sarkin ya ce ya rubuta takarda ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i domin ya kawo musu gudunmawar jami’an tsaro a yankin don magance matsalar.
Mukaddashin Shugaban karamar Hukumar Lere Alhaji Muhammad Sa’adu Kagarko ya jajanta wa al’ummar masarautar kan lamarin a zantawarsa da wakilinmu, inda ya bayyana aukuwar lamarin da abin takaici da tsoratarwa.
Ya bukaci jama’ar yankin cewa idan suka ga bakuwar fuska da ba su yarda ita ba, su sanar da jami’an tsaro.
Alhaji Adamu Garba, mijin matar da aka sace aka bar jaririnta, ya ce cikin dare a ranar Lahadi, sai suka fara jin harbe-harbe a gari. “Daga nan barayin suka zo gidana suka dauki matata wadda take goyon jaririya ’yar shekara daya da watanni. Har yanzu ba mu ji duriyarsu ba, don haka muna ta addu’a Allah Ya bayyanar mana da ita,” inji shi.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Zubairu Abubakar ta waya, amma bai same shi ba. Amma wata majiya a ofishin ’yan sandan garin Saminaka ta tabbatar da faruwar lamarin kuma sun tura maganar zuwa hedkwatarsu a Kaduna don daukar mataki.