Masu garkuwa da mutane sun sace wani babban jami’in gwamnati a Kaduna
Wasu gungu masu garkuwa da mutane sun sace wani babban jami’in gwamnatin ma’aikatar ilimi da kimiyya ta jihar Kaduna inda suka nemi kudin fansar Naira miliyan 40. Wani babban jami’i a ma’aikatar ilimin ne ya tseguntawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya haka. Masu garkuwa da mutanen sun sace Mista John Gorah a tsakar daren ranar […]

Wasu gungu masu garkuwa da mutane sun sace wani babban jami’in gwamnatin ma’aikatar ilimi da kimiyya ta jihar Kaduna inda suka nemi kudin fansar Naira miliyan 40.
Wani babban jami’i a ma’aikatar ilimin ne ya tseguntawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya haka.
Masu garkuwa da mutanen sun sace Mista John Gorah a tsakar daren ranar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke Mararaban Rido da ke jihar Kaduna.
Matimakin Daraktan a Bangaren Ilimin Mai Zurfi na Ma’aikatar Ilimin, Mista Steven Haruna ya fada wa kamfanin dillacin labarai na Najeriya a Kaduna cewa wadanda suka yi garkuwa da shi sun tuntubi iyalansa.
Haruna ya ce masu garkuwa da mutanen sun yi wa gidansa dirar mikiya, suka rika harbin iska don su tsorata jama’a, daga bisani suka rusa wani bangare na katangar gidansa sannan suka yi awon-gaba da shi.