Masu garkuwa da ni Fillancin kasar Nijar da Chadi suke yi – Wanda aka sace

Dan kasuwar ya ce akasarin masu garkuwar Fulani Nijar da Chadi ne

Masu garkuwa da ni Fillancin kasar Nijar da Chadi suke yi – Wanda aka sace

Masu garkuwa da mutane

A ’yan kwanakin nan, wasu masu garkuwa da mutane sun sako wani dan kasuwa a jihar Kano bayan biyan kudaden fansa. A cikin tattaunawar sa da Aminiya, mutumin, wanda bai amince a ambaci sunan sa ba, ya yi bayani kan abubuwan da suka wakana yayin garkuwar da shi, inda ya ce wasu daga cikinsu ’yan kasar Nijar da Chadi ne saboda irin Fillancin kasashen suke yi.

Ko za ka iya fada mana abinda ya wakana ranar da aka sace ka a takaice?

Ranar da abin ya faru, ranar wata Talata da misalin karfe 2:30 na dare na jiyo harbe-harben bindiga. Sai na tashi domin na gano me yake faruwa.

A lokacin ne wani kane na ya kira ni a waya yana tambaya ko a gida na ne ake harbe-harben na ce masa a’a, ashe ban san sun zo dab da gidan nawa ba.

Ina da matsalar idanu, saboda haka ba na gani sosai, sai na tashi na yi alwala na yi sallah. Sai na ji karar harbe-harben bindigar ya dada karuwa, wanda daga bisani na gano musayar wuta ake yi tsakanin ’yan bindigar da ’yan sanda.

Daga nan sai na ji harbe-harben sun tsagaita na kamar tsawon mintuna 20, sai na yi zaton sun tafi. Kawai sai ji na yi suna hawa kan saman masallacin dake kusa da gida na.

Sai na tashi na saka kaya na na zo kusa da kofa. A lokacin har sun ma fara haurowa cikin gidan nawa. Sai suka balle kofar shigowa falon gidan da kuma taga suka hawo kan benen da nake kwana.

Sai suka ce na bude musu kofar daki na ko su balle ta. Sai na bude musu, sai suka tambaye ni ko ina da manyan kudade a ciki, sai nace musu a’a, sai suka ce za su tafi da ni.

Suka ce tunda dai ni dan kasuwa ne dole ina da kudi ko a shago, amma na ce musu ba ni nake zama a ciki ba, bani da tabbas ko za a samu.

Da suka fito da kai daga gidan, me kuma ya faru?

Da muka fito, sai suka ci gaba da harbe-harben. Suka umarce ni in kwanta. Uku daga cikinsu kuma suka ci gaba da musayar wuta da ’yan sanda, a nan ne kuma suka sami nasarar kona wata motar ’yan sanda wadanda suka ce suna kawo musu tarnaki a harkarsu.

Daga nan ne sai suka ajiye baburansu muka yi tattaki na kamar kilomita daya, ban ma san inda muke tafiya ba.

Sai suka kaimu gefen wata gona suka ajiye mu a ciki, kafin mu ci gaba da tafiya daga baya.

Muka koma kan wata babbar hanya, muka ci gaba da tafiya, har muka je wani gida mai katon get, inda suka shigar da ni ciki tare da wasu mutum uku muka kwana a ciki.

Daga ciki ina jin karar motoci da dabbobi suna wucewa ta bayan gidan.

Ku nawa aka ajiye a cikin gidan?

Ni kadai ne na kwana a cikin dakin da aka ajiye ni. Sun ce min akwai wani dakin da wasu mutanen a ciki, amma dai ina zrgin kamar ni kadai ne a ciki.

Shin sun ba ka abinci a gidan?

Da gari yaw aye, kamar misalin karfe 7:00 na safe sai suka tashe ni suka ce mu fara cinikin kudin fansa.

Na tambaye su su bani ruwa na kuskure baki na amma suka ki, na ce musu zan yi sallah amma suka hana ni, wai ina cikin uzuri.

Da na ga daya daga cikinsu ya yi alwala zai yi sallah sai na tambaye su me yasa ni suka hana ni, sai suka ce shi yana da ’yanci amma ni bani da shi.

Suka hana ni ruwa domin yin alwala, suka ce sai dai na yi Taimama da kasa. Haka muka ci gaba har kusan Azahar, inda a nan suka yarda suka bani ruwa na kuskure baki na.

Sai suka bani burodi, sannan suka kira waya suke shaida min a lokacin garinmu na can cike da ’yan jarida da ’yan kallo suna ta surutun banza.

Duk abinda yake faruwa a garin a lokacin a kunnensu yake, suna da masu ba su bayanai.

Sun ma yi barazanar kai ni wani daji a Jamhuriyar Nijar matukar na ki ba su hadin kai ta hanyar biyan kudin da suke nema.

Kashegari sai suka bani waya suka ce na kira ’yan uwa na su kawo manyan kudade. Sun ma yi barazanar ko dai su kashe ni, ko su cefanar da ni ga wasu masu garkuwar da suka fi su hatsari ko kuma su sayar da ni ga masu amfani da mutane.

Da gari ya sake warewa ranar Alhamis sai muka fara ciniki. A lokacin wayoyinsu babu kudin kira ma, sai da suka jira suka sami kudi wadanda suka yi amfani da su wajen sayen kati da kuma taliyar da suka girka mana.

Lokcin da kake tsare a hannunsu, sun taba dukanka?

A’a, ba su doke ni ba. Sai dai kawai lokacin da muke ciniki na ki amincewa da farashinsu sun yi barazanar za su bar ni da yaransu su azabtar da ni.

Sun ce wai sai na basu Naira miliyan 100, inda na ce musu ban ma taba mallakar wannan kudin ba a rayuwa ta.

Sai wani daga cikinsu da ake kira Kwamanda Falalu ya daure hannu na na hagu da igiya saboda dama na riga na sami gocewar kashi a hannu na na hagu sakamakon faduwar da muka yi a kan babur lokacin da suka tafi da ni.

Dalilin daure hannun da suka yi, sai ’yan yatsu na suka kukkumbura saboda jini ba ya gudana. Da na ji azaba ta kai azaba, sai na kara musu miliyan daya a kan farasahin, amma duk da haka suka ki yarda, na kara biyu, uku, har aka kai karin biyar… a haka a haka har sai da muka kai farashin da suka amince sannan suka fara kiran ’yan uwa na domin tattauna yadda za a kawo musu.

Yawancin wadanda suka dauke ni daga gida na ’yan Najeriya ne, saboda na gane irin Fillancin ma da suke yi, ba su ma da nisa daga garinmu. Na san Fulanin Kamaru, na san na Nijar, na Chadi da ma na Najeriya.

To su wadanda suka dauke ka din wanne irin Fillanci suke yi?

Akwai ’yan Najeriya a cikinsu, akwai kuma baki. Bakin ’yan kasashen waje ne suke hada kai da Fulaninmu na nan gida su sato musu masu kudi, su kuma su sallame su. Na san Fillanci sosai kuma ina gane na kowanne yanki.

A wanne irin abin hawan suka zo lokacin daukar ka?

Dukkansu a kan Babura suka zo.

Ko za ka iya tantance yawan baburan?

To, ka san nace maka ina da matsalar idanu, amma duk da haka zan iya kiyayewa na ga Babura kamar biyar zuwa shida a lokacin.

To yaya aka yi suka sake ka?

Da suka amince da farashin da zan biya daga karshe sai suka ce min, “Tsoho, yau a gida za ka kwana. Mutanenka na can na kokarin hada kudaden.”

Wajen lokacin sallar Azahar sai suka firgita ni tare da umartar masu gadi na su kara tsaurara tsaro.

Da jin haka, sai na yi tsammanin ko watakila har yanzu ba su gamsu da farashin ba ne ko kuma suna tsoron za a biyo sahunsu ne.

Sai suka sake shirya bindigoginsu. Bayan faduwar rana, sai suka kyale ni na yi sallolin Magariba da Isha, inda suka ce a lokacin za mu tafi, amma suka gargade ni idan na kuskura na ga jama’a na yi ihu idan muka zo wucewa ta wani gari za su kashe ni.

Suka ce min ka san dai babu wani garin da zai fi karfinmu, muna da bindigogi. Sai na ce musu ba zan yi ihu ba.

Sai suka bani wata riga suka ce na canza saboda ta jiki na ta yi datti sakamakon ita ce a jiki na tsawon kwanaki ukun da suka kama ni, sannan kuma jikinta akwai jini saboda raunin da na ji lokacin da muka fadi daga kan babur. Suka bani wata rigar atamfa na sa.

To a ina suka ajiye ka bayan sun sako ka?

Da muka baro gidan bayan sallar Isha, sai muka yi tafiyar kamar mintuna 15 zuwa 20 a daji, sai muka hau kan wata hanyar birji wacce ta kaimu zuwa wani kauye, inda a nan ne suka kira abokan aikinsu domin su tabbatar an biya kudin fansar.

Har kiran waya suka hada tsakaninsu da ’yan uwa na, masu karbar kudin da kuma ni a lokaci guda.

Da suka tambayi masu karbar kudin inda ya kamata su ajiye ni, sai suka ce musu su kai ni wani kauye da ake kira Kirya a karamar humumar Babura ta jihar Jigawa.

Daga nan ne sai muka dauke hanya zuwa cikin wani daji, ban ma san inda muka dosa ba.

Sai muka sake faduwa a kan babur din da muke, daga karshe kawai sai suka ce ko ma a ina ne kawai su jefar da ni. Sai suka jefar da ni a gefen hanya suka tafi.

Na tsaya a wurin kamar tsawon mintuna 30, amma duk mai babur din da na tsayar ba ya yarda ya tsaya.

Akwai wani da na tsayar har sau uku yaki tsayawa, da ya ga duk zuwa sai ya dawo ya same ni tsawon wannan lokacin sai ya amince ya dauke ni inda ya kai ni wani gari na shaida musu abinda ya faru da ni.

To yaya za ka bayyana iftila’in gaba dayansa?

Na dauke shi a matsayin kaddara, kuma ina godewa Allah da ya kubutar da ni. Ina godiya ga jama’a saboda addu’o’in da suka rika yi min, da ma ’yan sanda da suka yi matukar kokari wajen ganin ba a tafi da ni ba a karon farko.

Na kuma godewa kafafen watsa labarai kan yadda suka baza labarin domin mutane su ji kuma su yi min addu’a. Nagode sosai.

Shin mutanen da suka sace ka manya ne ko matasa?

Biyu daga cikinsu matasa ne masu kimanin shekaru 20 zuwa 22, yayin da sauran kuma manya ne ’yan kasashen Nijar da Chadi. Kuma manyan cikinsu sun iya harbi sosai, sun san yadda ake sarrafa bindiga yadda ya kamata.

Kamar su nawa ne a kan babur din lokacin da suka dauke ka?

Akwai Babura biyu ne suka tafi da ni a alokacin, kowanne yana dauke da mutum daya, yayin da shi kuma wanda nake kai aka saka ni a tsakiya, kowannensu yana dauke da bindiga.

Sun ma nuna min irin bindigar da suke amfani da ita.

Sun ce akwai irin bindigogin ’yan sandan Najeriya, akwai kuma manyan bindigogi  wadanda ake amfani da su a yaki, wadanda suka ce za su iya yin nisan zangon kimanin kilomita biyu idan aka harba su, sun ce da irin su suke amfani.