Masu garkuwa da Olu Falae sun shiga hannu
Hukumar tsaro ta farin kaya ta gabatar da mutum biyu daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwar da Cif Olu Falae a gaban manema labarai a Abuja.Mutanen biyu su ne Abdullahi Usman, wanda aka fi sani da Kadiri) da Babaworo Kato, sun kuma amsa zargin da ake musu. Da yake gabatar da su, […]
Hukumar tsaro ta farin kaya ta gabatar da mutum biyu daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwar da Cif Olu Falae a gaban manema labarai a Abuja.
Mutanen biyu su ne Abdullahi Usman, wanda aka fi sani da Kadiri) da Babaworo Kato, sun kuma amsa zargin da ake musu. Da yake gabatar da su, jami’in hukumar, Abdullahi Garba ya bayyana cewa am damke su ne a otel din J. Zebra Hotel da ke Lokoja. Ya kara da cewa garkuwar da aka yi da Falae ba ta da alaka da kasancewarsa muhimmin mutun a kasar ko kasancewarsa shugaban kabilun Yarabawa. A cewarsa, wadanda suka yi garkuwar ’yan ta’adda ne kawai da ke yin garkuwa domin karbar kudin fansa, a saboda haka ya ja hankulan ’yan Najeriya da su guji yin duk wani abu da ka iya janyo rikicin kabilanci, ka na ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta raga wa duk wani da aka samu da son tayar da tarzoma ba.
Shugaban kungiyar Miyyati Allah, reshen Jihar Ondo, Alhaji Bello Garba ya shaida wa Aminiya cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kame mutun 4 a garin Ekiti da mutum guda a Neja, wadanda su ma ake zargi da hannu a yin garkuwar. “Jami’an tsaro ne suka gayyato ni na zo na gan su, bayan sun kawo su Jihar Ondo. Na tambayi wadanda suka yi garkuwar mene ne sana’arsu kuma ina shanunsu? Sai suka ce mani su ba su da sana’a, ba su kiwo domin ba su da shanu. Na tambaye su to ya aka yi suka yi garkuwa da Falae kuma daman sun san shi ne? Sai suka ce ba su san shi ba, akwai wasu mutane 2 Yarabawa ne suka nuna masu gonar Olu Falae amma kafin su yi garkuwar sai suka koma. Na tambaye su ko sun san gidan mutanen sai suka ce wadanda aka kai Abuja ne suka san gidan, da su ma sun sani da sun nuna wa ’yan sanda. Sun bayyana mani cewa bayan sun yi garkuwa da shi a gonarsa da ke Akure North sai da suka bari dare ya yi tukunna suka tafi da shi dajin karamar Hukumar Owo, inda suka yi garkuwar da shi. Daga daya bangaren kuma, akwai wadanda ke Jihar Neja, ciki har da wanda aka kama a can mai suna Dattijo; su ne suka dinga magana da iyalan Falae game da kudin fansar, bayan da aka ba su Naira miliyan 5 sai suka kira su ta waya suka ce su sake shi, an ba su kudin.
“Na tambaye su, me ya sa su ba makiyaya ba za su zo su shafa wa Fulani makiyaya kashin kaji har su janyo ana cewa za a kore mu? Sai suka ce mani su kawai suna yin garkuwa ne domin a ba su kudin fansa.”
A cewar Bello Garba, mutum 4 da aka damke a Ekiti su ne Hassan, Idris, Umar sai Masa’ud sai kuma wanda aka kama a Neja, wanda ya ce sunansa Dattijo. Za dai a gurfanar da su a gaban kuliya a Jihar Ondo.