Masu garkuwa na neman N30m kan yara 3 a Kaduna

’Yan bindiga na neman miyagun kwayoyi da kayan abinci da kudi Naira miliyan 30 kafin su sako yara uku ’yan gida daya da suka sace a Kaduna

Masu garkuwa na neman N30m kan yara 3 a Kaduna

Kananan yaran da suka kubuto daga hannun masu garkuwa. (tsohuwar ajiya).

’Yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu yara uku a Jihar Kaduna na neman kudin fansa Naira miliyan 30.

A makon jiya ne ’yan bindiga suka kutsa gidan wani likita suka yi awon gaba da ’ya’yansa uku a unguwar Azala da ke yankin  Katari a Karamar Hukumar Kachia.

Wani makusancin iyalan likitan mai suna Barnabas, ya ce, “Iyalan sun shiga tashin hankali saboda rashin samun tuntuba daga masu garkuwar.

“Sai a ranar Asabar da misalin 11 na dare shugaban masu garkuwar ya kira yana neman kudin fansa Naira miliyan 30 da kayan abinci da kwaya kafin su sako yaran.”

A cewarsa, iyalan sun roki a sassauta kudin zuwa abin da za su iya.

Kawo yanzu kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, SP Hassan Mansur, bai yi tsokaci kan lamarin ba.

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai