Masu garkuwa sun dauke matar shugaban matasa

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da matar Shugaban Kungiyar Matasan Kabilar Eggon Daniel Anyabuga a jihar Nasarawa. Maharan dauke da bindigogi sun shiga gidan shugaban matasan ne da dare inda suka tafi da matar mai suna  Ruth Asheahe Daniel zuwa wani wuri da ba a sani ba. Da yake tabbattar da aukuwar […]

Masu garkuwa sun dauke matar shugaban matasa

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da matar Shugaban Kungiyar Matasan Kabilar Eggon Daniel Anyabuga a jihar Nasarawa.

Maharan dauke da bindigogi sun shiga gidan shugaban matasan ne da dare inda suka tafi da matar mai suna  Ruth Asheahe Daniel zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Da yake tabbattar da aukuwar hakan ga wakilin Aminiya, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa Bola Longe ya ce rundunarsa ta kama mutun hudu bisa zargin garkuwa da matar sannan an kama babur din da aka yi amfani da shi wajen tafiya da ita.

A cewar Kwamishinan ‘yan sandan, biyu daga cikin wadanda aka kama makiyaya ne sauran kuma ‘yan asalin yankin da aka yi garkuwa da matar ne.

Ya kuma ce rundunarsa na kokarin cetowa tare da mayar da wadda aka yi garkuwa da itan ga iyalanta.

Hakazalika ya bukaci jama’a mussamman mazauna jihar da su taimaka wa ‘yan sanda da bayanan da za su taimaka a ceto matar.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutane ba za su sami mabuya a jihar Nasarawa ba, domin ‘yan sanda na aiki ba dare ba rana domin yakar ayukansu.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos