Masu garkuwa sun harbi jarogan APC sun sace ’ya’yansa a Abuja

’Yan bindiga sun harbi wani jagoran Jam’iyyar APC tare da yin awon gaba da ’ya’yansa biyu da wasu makwabtansa a Abuja.

Masu garkuwa sun harbi jarogan APC sun sace ’ya’yansa a Abuja

’Yan bindiga sun harbi wani jagoran Jam’iyyar APC tare da yin awon gaba da ’ya’yansa biyu da wasu makwabtansa a Abuja.

A daren ranar Litinni ne maharan dauke da bindigogi kirara AK-47 suka kutsa gidan Alhaji Musa Majaga da ke unguwar Yangoji a Karamar Hukumar Kwali.

Wani dan unguwar Yangoji mai suna Abdullahi ya ce lamarin ’ya faru ne a da misalin karfe 12;23 na dare inda maharan suka lalata tagogin gidan suka shiga dakinshi suka harbe shi suka dauke ’ya’yansa biyu.

“Daga nan suka shiga gidan makwabtansa inda suka kara daukar wasu mutane uku,” inji shi.

Wani dan banga wanda da ya zanta da wakilinmu ya ce sai da masu ’yan bindigar suka lura ’yan banga na da karancin rashin harsashi suka kai harin.

“Sun kawo harin ne bayan da suka samu labarin cewa ’yan banga ba su da harsasai, inda suka yi awon gaba da mutane biyar.

“Idan ba haka ba, an kai watanni biyar rabon da a kawo hari a sace wani a nan Yangoji,” in ji shi.

Ya ce an kai jigon APC da aka harba a kafarsa wani asibiti mai zaman kansa da ke Gwagwalada domin yi masa magani.

Kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine, ta bukaci wakilinmu da ya ba ta lokaci domin jin yadda lamarin ya faru.

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump

An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47

Za mu yi gwanjon motoci 891 da muka ƙwace — EFCC