Masu garkuwa sun kashe matashi bayan karbar kudin fansa N16m

Sun harbe Abba ne a lokacin da wanda ke tattaunawa da su ya kai wa shugabansu Naira miliyan 16 da babura uku

Masu garkuwa sun kashe matashi bayan karbar kudin fansa N16m

’Yan bindiga sun harbe wani matashi mai shekaru 27 har lahira bayan sun karbi kudin fansar Naira miliyan 16 da babura uku domin sako shi da wasu mutane tara a Jihar Kaduna.

A ranar 16 ga watan Afrilu ’yan bindiga suka kutsa gidaje a uguwar Iya da ke garin Jere inda suka sace mutane tara sannan suka nemi kudin fansa Naira miliyan 30.

Wani mazaunin garin mai suna Shuaibu Hussaini ya tabbatar wa wakilinmu a wayar tarho ranar Laraba cewa masu garkuwar sun kashe Abba ne a ranar Asabar.

Shuaibu ya ce masu garkuwar sun harbe Abba ne a lokacin da wanda ke tattaunawa da su ya kai wa shugabansu Naira miliyan 16 da babura uku a wani wuri da suka yi alkawari.

A cewarsa, bayan ’yan bindigar sun karbi kudin da baburan ne shugabansu ya daure Abba da igiya ya bude masa wuta.

“Daya daga cikin wadanda ’yan bindigar suka sako ya ce shugaban masu garkuwar ya shaida musu cewa sun kashe Abba ne saboda taurin kai da ya yi musu a lokacin da ake tattauna kudin fansar.

“Da ’yan uwan wadanda aka sako suka nemi Abba suka rasa bayan biyan kudin fansa ne shugaban masu garkuwar ya ce musu su je su dauki gawarsa,” in ji shi.

Hussaini ya ce kisan gillan da ka yi wa Abba ta jefa daukacin al’ummar Jere cikin damuwa.

Wakilinmu ya so samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, amma hakan bai samu ba.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji