Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja

’Yan ta’addan sun biyo sawun tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ne bayan ya ciro kuɗi a banki.

Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja

Ana fargabar cewa wasu masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya Zagazola Makama cewa ’yan ta’addan sun ɗauke Parradang a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar da safiyar wannan Talatar.

Makama ya ce ’yan ta’addan sun biyo sawun tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ne bayan ya ciro kuɗi a banki, inda suka karɓe kuɗin sannan kuma suka kashe shi.

Wannan lamari dai ya sake ɗaga hankalin mazauna Abuja a fannin tsaro musamman yadda a bayan nan ta’adar kashe-kashe da garkuwa da mutane ke ƙara ƙamari.

Parradang dai ya shafe fiye da shekaru 30 yana aiki a Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a faɗin ƙasar cikin har da kujerar Kwanturola-Janar na ƙasa.

Ya yi aiki a jihohin Kano, Legas, Kwara, Enugu da Abuja, sannan ya yi kwasa-kwasai na neman ƙwarewa da sanin makamar aiki a nan cikin gida da ƙetare.

Tuni hukumomin tsaro suka soma gudanar da bincike domin bankaɗo masu hannu a wannan aika-aikar.

Kawo yanzu babu wata sanarwa da hedikwatar Hukumar Shige da Ficen ta fitar dangane da faruwar lamarin.

Sai dai wani jami’anta a hedikwatar da ke Abuja ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa a jira hukumar ta fitar da sanarwa a hukumance.