Masu garkuwa sun sace mutane 56 a Jihar Neja
Sun bai wa mazauna ƙauyukan wa’adin ranar 15 ga watan Yuni a matsayin ranar karɓar kuɗin fansa
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 56 a kananan hukumomin Munya da Shiroro da ke Jihar Neja.
Mutum 30 an sace su ne a unguwar Kakuru da ke Karamar Hukumar Munya, sauran 26 kuma a yankunan Adogo Mallam da Tunga Kawo a Ƙaramar Hukumar Shiroro.
An sace mutanen ne a ranakun Lahadi da Litinin a unguwanni daban-daban a jihar.
Yankin Kakuru da aka sace mutane 30 na da tazarar kilomita biyar daga yankin Kuchi inda aka sace mutane 150 a makon jiya.
- An kama ɗan bindiga mai shekara 70 a Kaduna
- Amarya ta yanke mazakutar angonta bayan wata hudu da aurensu
- Hajjin Bana: An kammala jigilar alhazan Kaduna sama da 4,000
’Yan bindigar da suka sace mutane 150 daga yankin Kuchi suna neman kuɗin fansa Naira miliyan 150, kuma sun ba iyalan waɗanda aka sace wa’adin ranar 15 ga watan Yuni su biya kuɗin ko su kashe biyar daga cikin waɗanda aka sace.
’Yan bindigan sun kuma yi barazanar za su riƙa kashe mutanen da ke hannunsu a kullum har sai an biya kuɗin fansa.
Amma sun sako wani mutum da matarsa da ’ya’yansa huɗu a cikin waɗanda suka sace, cewa ya je ya nemo Naira miliyan 60 domin a sako ’yan uwansa.
Majiyar kafar The Nation ta ruwaito cewa tun farko jama’ar yankin sun bayar da N60,000 domin a sako wadanda aka sace, amma ’yan ta’addan suka ƙi amincewa.
Daga baya al’umnar sun kara kuɗin zuwa N100,000 amma duk da haka ’yan bindigar suka ƙi amincewa.
Wata majiya a yankin ta ce ’yan bindigar sun yi iƙirarin cewa kuɗaɗen da jama’ar ke bayarwa ba su kai abin da suke hayar bindigogi ko sayen harsasai ba, tare da bayyana cewa ba za su rage kuɗin fansan da suka nema ba.