Masu garkuwa sun sako mahaifiyar dan wasan Super Eagles
Masu garkuwa da mutane da suka kama mahaifiyar dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bordeaud da ke kasar Faransa, Samuel Kalu, wato Uwargida Ozuruonye Juliet Kalu sun sako ta. Masu garkuwar da mutane sun kama ta ce a watan jiya, inda aka biya su kudin fansa […]
Masu garkuwa da mutane da suka kama mahaifiyar dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bordeaud da ke kasar Faransa, Samuel Kalu, wato Uwargida Ozuruonye Juliet Kalu sun sako ta.
Masu garkuwar da mutane sun kama ta ce a watan jiya, inda aka biya su kudin fansa Naira miliyan uku, amma suka ci gaba da tsare a dattijuwar, suna neman sai an kara musu wasu kudin kafin su sako ta.
Aminiya ta samu labarin cewa masu kama mutane suna garkuwa da su sun kama Juliet Kalu ne a ranar 27 ga watan Fabrairu da ya gabata a kauyen Umuamacha da ke Karamar Hukumar Umueze da ke Jihar Abiya, lokacin da take kan hanyarta ta komawa gida. Wakilinmu ya kalato cewa dan wasa Samuel Kalu ya shaida wa jaridar Sportinglife cewa tun farko sai da suka ba masu garkuwa da mahaifiyar tasu Naira miliyan uku, bayan sun amshi kudin kuma suka ce lallai sai an kara musu Naira miliyan goma sha uku. “Da farko sun bukaci mu ba su Naira miliyan uku, muka bayar. Muna sa ido mu ga dawowarta gida, sai muka yi ta jira shiru, ba amo ba labari, sai muka hakura,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, bayan sun shafe daren da suka bayar da kudin ba su ji motsin mahaifiyar tasu ba, washegari masu garkuwar sun kara kiransu, suka ce wadancan kudin ba su aka ba ba, an yi kuskure an ba wani; ba su ba. Don haka yanzu sai an ba su Naira miliyan goma sha biyar.
Dan wasan ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Abiya ya san da maganar, kuma da su aka yi ta kokarin ganin an kubutar da ita.